Tun bayan komawar Ruben Amorim kungiyar kwallon kafa ta Manchester United yake fuskantar kalubale kala-kala musamman na rashin nasara da kuma labarin fitar ‘yan wasa 11 na farko da za su buga wasan da kungiyar ta doke Manchester City a filin wasa na Ettihad, laifin da aka dora shi a kan ‘yan wasa Alejandro Garnacho da Marcus Rashford da kuma Amad Diallo.
Kawo yanzu Manchester United ta yi rashin nasara a wasanni 10 cikin wasanni 22 da ta buga wanda hakan ya sa take zaune a mataki na 12 a kan teburin gasar duk da cewa tana kokari a gasar cin kofin Europa League amma hakan ba shi yake nuna cewa komai yana tafiya daidai ko yadda ya kamata ba a kungiyar kuma ya nuna yadda gagarumin aiki yake kan kociyan kungiyar.
- Kasar Sin Ta Harba Sabon Tauraron Dan Adam Na Gwaji A Kan Fasahar Sadarwa
- ‘Yan Nijeriya Za Su Maka Gwamnati A Kotu Kan Karin Kudin Kiran Waya
Cikin fushi bayan tashi daga wasan da kungiyar tta yi rashin nasara a hannun kungiyar Brighton Albion da ci 3-1 mai koyarwa Ruben Amorim ya ce watakila wannan ce kaka mafi muni a tarihin kungiyar a Premier League kuma hakan ne ya sa United tana ta 13 a teburin gasar ta Ingila da maki 26, kuma ya bayyana cewa nan gaba kungiyar za ta ci gaba da yin rashin nasara.
Wane Mummunan Tarihi Kungiyar take kafawa?
Bayan da Brighton ta yi nasara a kan Manchester United a filin wasa na Old Trafford, karo na shida kenan da aka doke kungiyar a gida a wasa na 12 tun bayan 1893/94. United ta kare a karshen teburi, lamarin da ya kai ga ta bar buga gasar ta rukunin farko a lokacin da ake kiranta da sunan Newton Heath.
A shekarar 1914/1915 aka sauya sunan kungiyar zuwa Manchester United, wadda ta kare a gurbi na 18 a cikin kungiyoyi 20 – da maki 30 a karawa 38 kuma wani rashin kokarin da United ta yi a kakar shi ne lashe wasa tara wato kaso 24 cikin 100, idan ka kwatanta da 32 cikin 100 a kakar nan sannan sau biyar jimilla United tana zuwa fadowa daga buga gasar Firimiya a Ingila, wadda ta yi ta karshe a 1921/22 da maki takwas da kara yin ta karshe a 1930/31 da maki 10.
Manchester United ta taba komawa buga gasar rukunin farko da faduwa daga wasannin a 1935 da kuma 1938 – kaka ta baya-baya ita ce 1973/74 lokacin da ta kare ta 21 daga kungiyoyi 22, har ila yau wannan ce kaka mafi muni a United da take ta 13 a kan teburi tun bayan 1989/90 da take kan irin wannan matakin kuma kungiyar da Amorim ke jan ragama tana da maki 26 daga wasa 22, wato tazarar maki takwas daga rashin kwazo a gasar baya.
Manchester United ta hada maki 34 a 2019/20 a irin wannan lokacin, amma sai ta kara kwazo da ta kare a mataki na uku da maki 66 kuma bayan hada maki 35 daga karawa 22 a bara, United ta kare a mataki na takwas da maki 60 da lashe FA Cup karkashin tsohon kociyan kungiyar da ta kora, wato Erik ten Hag. Haka kuma United ta kare kakar Premier League a mataki na shida karo uku da yin ta bakwai a 2013/2014. Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta dauki kofin Premier League 13 daga kaka 21 karkashin tsohon kociyan kungiyar wato Sir Aled Ferguson, wannan ce kaka ta 12 rabon ta da lashe babbar gasar firimiya ta Ingila, tun bayan da ya yi ritaya duk da irin makudan kudaden da kungiyar ta kashe a lokutan Erik ten Hag da Dabid Moyes da Jose Mourinho da Luis Ban gaal da Ole Gunner Solkjaer.