Assalamu alaikum, dan Allah Malam Ina bukatar bayani a kan bambancin wadannan Ruwan guda biyu masu fitowa daga gaban mace, watau “KUDRA da kuma SUFRAH”? Allah ya saka da alkhairia.
Wa’alaykumussalam. To ‘yar’uwa, wannan yana daga cikin mas’aloli masu mutukar muhimanci, amma ga abin da ya sawwka game da haka :
Sufra na nufin mace ta ga ruwa mai fatsi-fatsi kamar ruwan ciwo, ya fito daga gabanta.
Kudra kuwa na nufin: ruwa ya ringa fitowa daga farjin mace, wanda kalarsa take kasancewa tsakanin fatsi-fatsi da baki wato kamar ruwa gurbatacce.
Dangane da hukuncinsu kuwa: idan daya daga cikinsu ya kasance a tsakiyar haila ne ko kuma yana hade da haila kafin ta sami tsarki to wannan ana saka shi a cikin haila, idan kuma bayan tsarki ne to ba haila ba ne saboda fadin Ummu Adiyya “mun kasance ba ma kirga sufra da kudra bayan tsarki a cikin haila”, Abu Dawud ya ruwaito shi da sanadi mai inganci.
A hadisin A’isha kuma (Mata suna aiko mata da abin da suke sawa lokacin da suke haila a jikinsa akwai sufra (wato ruwan da yake kama da ruwan ciwo) sai ta ce musu kada ku yi gaggawa har sai kun ga farin ruwa ya fito, ta yadda za mu yi amfani da hadisin Ummu Adiyya bayan an sami tsarki, ma’ana ko ta ga sufra da kudra ba za ta kirga su a cikin haila ba, hadisin A’isha kuma za mu yi amfani da shi idan tana cikin haila ta yadda za ta kirga da su.
Allah ne mafi sani.
A Karshen Dare Ake Yin Wutiri
Assalamu alaikum wa rahmatullah. Malam mene ne hukuncin yin wuturi a lokacin taraweeh bayan kuma mutum yana son yin tahajjud cikin dare?
Wa’alaikum assalam, in har mutum ya san zai yi wata sallar bayan tarawihi, to abin da yake daidai shi ne ya jinkirta wutirinsa zuwa karshen dare saboda hadisin da Bukari da Muslim suka rawaito cewa: Annabi (SAW) yana barin wutirin sa in ya yi sallar dare zuwa lokacin sahur, da kuma hadisin da Annabin yake cewa: Ku sanya wutiri sallarku ta karshe da daddare”
Bukari ne ya rawaito da Muslim.
Allah ne mafi sani.
Mene Ne Hukuncin Wanda Ya Kashe Kansa Da Gangan?
Assalamu alaikum, Malam mene ne hukunci da matsayin wanda ya kashe kansa ko ya yi sanadiyyar mutuwarsa da kansa, Allah ya kara wa malam ilimi da lafiya. Na gode.
Wa’alaikum assalam, wanda ya kashe kansa da gangan, ranar Alkiyama zai shiga wuta, zai ci gaba da kashe kansa da abin da ya kashe da shi a duniya a cikin wutar lahira mai kuna, kamar yadda ya tabbata a hadisi.
In har ya mutu da imani ko da kwayar zarra ne, ba zai dawwama a cikin wutar ba, zai fita bayan ya gama lokacin da Allah ya diba masa, kamar yadda hadisai suka bayyana.
Allah ne mafi sani.