“Anniyar Sin ta bude kofa ga waje, da inganta budadden tattalin arzikin duniya, ta faranta mana rai kwarai da gaske.” Wasu manyan jami’an kamfanonin kasashen waje kamar shugaban kamfanin Pfizer China, Jean-Christophe Pointeau, da shugaban kamfanin L’ORÉAL, Jean-Paul Agon, su ne suka bayyana hakan a wurin baje kolin kasa da kasa na hajojin da ake shigowa da su kasar Sin ko CIIE karo na 7. Sun kara da cewa, ana gudanar da baje kolin CIIE ko wace shekara, wanda ya kara kuzari ga kasa da kasa wajen yayata damammakin ci gaban Sin, sannan kuma ya kara anniyarsu ta habaka jarinsu a kasuwar Sin.
Shi kuma shugaban kamfanin SHISEIDO China, Toshinobu Umezu, ya bayanna cewa, a cikin shekarun da suka gabata ya shiga baje kolin CIIE, ya fahimci babban karfin wannan dandali. Ya ce bayan sun baje kolin sabbin fasahohi da sabbin kayayyakinsu, sun samu kulawa da karramawa daga masu sayayya, lamarin da ya shaida cewa, an cimma nasarar mayar da “kayayyakin da aka nuna” zuwa “kayayyakin da aka sayar”.
Bugu da kari, alkaluma sun nuna cewa, a cikin baje kolin CIIE guda shida da aka gudana, an nuna sabbin kayayyaki, sabbin fasahohi, da sabbin ayyuka kusan 2,500, kana jimillar darajar kwangilolin da aka daddale ta zarce dalar Amurka biliyan 420, wanda ya samar da karin damammakin ci gaba ga kamfanonin kasashen waje.(Safiyah Ma)