Kocin tawagar ‘yan wasan tawagar Argentina, Lionel Scaloni ya ce dan wasa Lionel Messi ya sha gaban Diego Maradona a matakin fitatcen dan wasan kwallon kafa na duniya.
Scaloni ya ce idan an bani zabi a tsakaninsu Messi zan zaba, domin yana da wasu abubuwa na musamman a tare da shi sabpda shi ne fitatcen dan kwallo a duniya, koda yake Maradona ma ya yi fice kamar yadda Scaloni ya yi hira da gidan radiyon Cope a Argentina ranar Talata.
- ’Yar Kasuwa Elizabeth Homes: Labarin Tashe Da Rushewarta (I)
- Dole A Hada Karfi Wajen Dakile Bazuwar Makamai A Afirka –Buhari
Mutane a Argentina sun fi kaunar Maradona fiye da Messi, sai dai watakila a samu sauyi nan gaba, bayan da dan wasan Paris St Germain ya ja ragama da Argentina ta lashe kofin duniya a Katar.
A watan jiya Argentina ta dauki kofin duniya na uku jumulla, kuma na farko tun bayan da Maradona yaja ragamar kasar ta lashe a shekarar 1986 sai dai a shekara ta 2014 taje wasan karshe inda tayi rashin nasara a hannun kasar Jamus.
Scaloni ya ce ya samu damar magana da Messi a lokacin da aka nada shi kociyan Argentina a 2018, inda ya rarrashi dan wasan PSG bayan da kasar ta kasa kai bante a gasar kofin duniya a Rasha.
Ya ce ”Abin da muka fara yi shi ne kiran waya ta bidiyo da Messi, kuma ya ce an martaba shi, abin da na fara sanar da shi cewar muna bukatarsa kuma haka kuwa aka yi ya dawo wasa bayan wata takwas muna jiranshi daga nan muka samu nasarar da muke bukata.”
Ya kara da cewa ”Horar da Messi ba abu bane mai wahala saboda babu yadda za kayi ka ci gyaransa, domin kwararre ne, wani lokaci za ka shawarce shi ya kara sa matsi – idan yana kan ganiya ba magana.”
Haka kuma Scaloni ya kare mai tsaron ragarsa, Emiliano Martinez kan yadda aka yi ta caccakarsa bisa dabi’a da ya nuna a lokacin da ya karbi kyautar mai tsaron ragar da ba kamarsa a Katar.
Haka kuma mai tsaron ragar ya rike ‘yar tsana mai fuskar Kylian Mbappe a lokacin da Argentina ke zagaye birin a budaddiyar mota inda ya ce akwai wasu halaye da ya nuna shi kansa zai yi dana sani, amma dai mai tsaron raga ne kwararre.