Tun lokacin da aka sanya hannu a dokar zabe da ake yi wa kuskwarima ta shekarar 2022 har ta zama doka, mutane suka fara hasashen cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) za ta iya gudanar da ingantaccen zabe wanda ba a taba irinsa ba a tarihin Nijeriya.
Ko da ma aka samu rahoton rashin tsaro zai iya sanyawa a dage zabe bai sauya tunanin shugaban hukumar ba. Mutane ma dai sun san cewa wannan ba huruminsa ba ne, akwai dan abu kadan da hukumarsa za ta iya yi.
- Dimokuradiyya Ta Zauna Daram A Nijeriya, Ba Batun Juyin Mulki – Shugaban Tsaro
- NIS Reshen Bayelsa Ta Fara Horar Da Jami’anta Kan Tsarin Aiki Da Sarrafa Makamai
Hukumar tana da wasu kalubale a tsare-tsarenta, amma wadannan matsaloli an magance su kuma zai iya faruwa a kowani lokaci, kuma a kowacce kasa. Matsalar da ake fama da shi wanda ya kamata INEC ta duba shi ne, yadda ‘yan siyasar Nijeriya suke zuzuta dabi’ar nan ta siyasar kabilanci da addini.
Sashi na 97 na dokokin zaben shekara ta 2022, ya zayyano cewa haramun ne yin yakin neman zabe a kan addini ko kabila. Dokar ta ce: duk dan takara koko wani mutum ko wata kungiya suka yi yakin neman zabensu a kan addini ko kabilanci ko bangaranci don sun tallata jam’iyyarsu ko su soki wani bangare ko dan takara sun aikata laifi a karkashin wannan sashi(a), wanda zai biya mafi yawan kudi na Naira miliyan 1,000,000 ko kuma a daure shi a gidan yari na tsawon shekar 12 ko kuma a hada mashi su gaba daya, sashi (b) idan kuwa jam’iyyar siyasa ta aikata wannan za ta biya mafi yawan kudi na Naira miliyan 10,000,000.
Wannan matsalar a nan idan aka danganta da jam’iyyar APC, wadanda suke amfani da wannan dama na cewa sun bayar da tikitin takararsu ga wadanda suke addininsu guda. A dokance kowa zai iya zabar wadanda suke addini guda don ma an yi a baya can, kenan wannan ba sabon abu ba ne. Zaben da aka soke na shekarar 1992 an yi tikitin musulmi da musulmi, inda Abiola da Kingibe suka yi takara a karkashin jam’iyyar SDP. Kafin takarar MKO, akwai takarar da aka yi na Kirista da Kirista a jamhoriya ta biyu a shekarar 1979, inda Cif Awolowo ya tsaya takara da abokin takararsa, Philip Umeadi, sai kuma Azikiwe na jam’iyyar NPP da abokin takararsa, Ishaya Audu. Dukkaninsu sun tsaya takara inda Shagari da Ekwueme da suke da tikitin musulmi da Kirista suka sami nasara.
Wannan tataburza na maganar tikitin musulmi da musulmi ya fara tashe ne a shekarar 2019, inda ya taso a matakin Jihar Kaduna. Tsarin dai jam’iyyar gwamnati ce ta tsara shi karkashin jagorancin El-Rufa’i don samun wata daman a kasancewar jihar musulmai sun fi yawa. Wannan ne ya haifar da sauya al’adar jihar na hada musulmi da kirista takara, inda aka koma tikitin musulmi da musulmi a Kaduna wanda hakan ya kara matsalar rashin tsaro. Duk da kiraye-kiraye mabambanta da ake ta yi a kan haka, amma jam’iyyar gwamnati ta yi watsi da wannan kiran, ba don komai ba sai don suna da son su sami nasarar zabe.
Lallai kuwa ‘yan siyasa suna yin tunanin daukan duk wani mataki da zai kai su ga nasara ba sa tunanin me zai dawo. Amma abun da yake nunawa karara shi ne ba sa tunanin talakawa da suke mulka kuma su ne masu zabe, bukatarsu shi ne samun nasara, misali a dauki Jihar Kaduna inda ake fama da matsalar tsaro wanda ya karu sakamakon amfani da addini. Darasin da ya kamata a dauka shi ne, yana nuna cewa duk da cewa yin tikitin musulmi da musulmi bai saba wa doka ba, amma a duba yanayin mutanen da suke zama a wurin.
Yin tikitin musulmi da musulmi ya sanya damuwa a zukatan kungiyoyin Kiristoci da suka hada da ita kanta CAN. Damuwar ita ce samun nasarar jam’iyyar APC yana da matukar wahala sakamakon mabiya addinin kirista da aka nuna masu cewa ba su isa ba, kuma mutane da dama suna tunanin tarihi ne zai maimaita kansa a kan abun da ya faru a shekarar 1979, inda wadanda suka tsayar da masu addini daya suka sha kaye.
Matsalar da aka samu shi ne, yadda wasu kiristoci suka ce su kuma nasu za su goyawa baya, wato Peter Obi. Wannan ya zo na bazata ko kuma tsararren shiri ne, amma kamar matakin bai karbu ba. Wata ziyara da Peter Obi ya kai coci an ji yana rokon mahalartar cocin da cewa su farka daga barci don su karbo kasarsu. A lokacin yakin neman zabe a Filato, wani Fasto ya ya yi kira ga kiristoci da su zo su karbi kasarsu. Wannan ma ya zama sababben sako, amma sakon ana daukansa karmar yanki-yanki ne wanda yake cikin ajandan al’ummar musulmi.
A bangarensu kuwa kungiyar Izala a wani taro da suka yi da gwamna Ganduje na Jihar Kano don su nuna goyon bayan tikitin musulmi da musulmi. Wani malami ya bayyana a cikin wani faifan bidiyo yana cewa tikitin musulmi da musulmi ya fi tikitin musulmi da kirista, sun fi mayar da hankalinsu kan tikiti ba wai matsalar tattalin arzikin kasa ba. Wani faifan bidiyo da aka yada da ke dauke da malamai suna taro, inda suke cewa zaben musulmi da musulmi kamar jihadi ne.
Dukkanin addinan nan suna zargin junansu kamar tsarin nan na karba-karba. Yakin neman zabe a kan addini iri daya ne, malamai da jagororin addini suna kiran magoya bayansu a kan su zabi wanda suke addini guda da su. Malamai da ‘yan siyasa suna magana ne a karan kansu ba sa duba alfanun jama’a kuma hakan da suke yi ya saba wa sahi na 97 na dokar zaben shekara ta 2022.
Idan aka yi la’akari da faya-fayan bidiyon da ake yadawa, ya zama wajibi hukumar INEC ta hukunta wadanda suka karya dokar. Kuma hukuncin wanda ya karya dokar an tanaje shi a karkashin dokar, kuma hakan zai sa a daina karya dokar. Abun mamaki sai INEC ta kawar da idonta a kan wannan. Shirun da ta yi yana nuna cewa INEC ko ta amince a karya dokar ko kuma ba ta san abun da dokar sahi na 97 yake nufi ba. Koma dai mene ne wannan bai kyautu ba ga hukumar. Ya kamata ta samar da dukkanin abubuwan da ake bukata wajen gudanar da zabe.
Jam’iyyun adawa sun fito fili sun bayyana abubuwan da ya shafe su. Jam’iyyu da suka shirya sun gudanar da ingantaccen yakin neman zabe don su sami kuri’a ba wai don su yi amfani da wata dama ba don kawar da tunanin masu zabe ta hanyar amfani da addini. Kamar Peter Obi ko Tinubu suna amfani da addini wajen yakin neman zabe.
Jam’iyyu da suke yakin neman zabensu a bisa al’adar da ake yi a baya na tikitin musulmi da kirista, kamar Jam’iyyar PDP za ta iya samun dama da matakan da wadannan suka dauka wanda hakan ya rarraba kuri’unsu.
A saboda haka, ya zama wajibi hukumar INEC ta yi hukunci ga duk wadanda suke karya doka ba don komai ba sai don ganin an sami ingantaccen zabe kuma karbabbe idan an sami tsaro. Idan ba haka kuwa, mutuncin hukumar da kuma na Buhari zai zube.