Shahararren dan wasan kwallon kafa mai taka leda a kungiyar Inter Miami ta kasar Amurka Lionel Messi.
Ya jefa kwallaye biyu rigis a wasan da kasarsa ta Ajantina ta samu nasara akan kasar Peru da ci 2-0.
Measi wanda ke cigaba da murmurewa daga raunin da ya samu a watan Satumba,ya zama dan wasan da yafi zura kwallaye a wasannin neman gurbin buga Kofin Duniya na kasashen Latin America.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp