Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya janye umarnin da ya bayar ga dukkan bankunan kasuwanci a ranar 6 ga Mayun shekarar 2024, inda ya umarce su da su aiwatar da cire kaso 0.05 cikin 100 daga duk wata hada-hadar kuÉ—i ta banki a matsayin harajin tsaron yanar gizo.
Umarnin cazar harajin ya janyo cece-kuce a faɗin ƙasar nan a lokacin da babban bankin ya gabatar da ƙudirin a makon da ya gabata, lamarin da ya sa fadar shugaban ƙasa ta dakatar da aiwatar da karɓar harajin na intanet.
- CBN Ya Yi Alkawarin Kawo Karshen Hauhawar Farashin Kayan Masarufi
- Za A Fara Rabon Takin CBN Kyauta, Sai Dai Masana Sun Ba Da Shawara
A wata sanarwar janye Æ™udirin da CBN ya fitar a daren Lahadi, ya umurci bankunan da dakatar da bin umarnin farko, kamar yadda shugaban Æ™asa ya buÆ™ata, hakan alama ce da ke nuna cewa gwamnatin mai ci tana saurare tare da bada fifiko ga koken jama’a.