Wani mutum mai shekaru 55 mai suna Olubunmi Johnson, ya shiga hannun ‘yansandan Jihar Ogun, bisa zargin kone matarsa da wuta a yankin Ota.
Rahotanni sun bayyana cewar lamarin ya faru misalin karfe 8:30 na daren ranar Juma’a, bayan wata sabani ya barke tsakanin ma’auratan a gidansu da ke kan titin Fagbuyi, Ilogbo.
- Ta Hanyar CIIE Duniya Ta Kara Fahimtar Matakan Sin Na Samar Da Abubuwa Da Aka Fi Tsananin Bukata
- Roma Ta Sallami Kocinta Ivan Juric Bayan Wasanni 12 Kacal
Ana zargin Johnson da zuba wa matarsa mai suna Kikelomo fetur sannan ya cinna mata wuta.
Kakakin ‘yansandan jihar, Omolola Odutola ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin.
Ta ce iyalan matar sun sanar wa ‘yansanda faruwar lamarin.
Odutola ta kara da cewa, duk da har yanzu ba a san musabbabin sabanin ba, amma an garzaya da matar asibiti.
Ta bayyana cewa an kama Johnson, kuma ‘yansanda na bincike kan lamarin a matsayin yunkurin kisa.
“Jami’an ‘yansanda daga ofishin Ilogbo sun yi gaggawar daukar mataki, inda suka kama wanda ake zargi mai shekaru 55.
“Shaidu sun garzaya da matar zuwa asibiti bayan ya cinna mata wuta,” in ji Odutola.