Assalamu alaikum masu karatu, barkan mu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Uwargida Sarautar Mata.
A yau shafin na mu zai ci gaba da kawo muku matsalolin gidan aure da yadda za’a magance su, a inda yau za mu yi magana kan dalilan da suka sa wasu maza ba sa hira da matansu.
Uwargida, ai ke ya kama ta ki fara yi masa hira kafin shi ya yi miki, wani sai an dauko masa hira sannan ya fara yi, da zarar kin dauko masa da hira idan ya fara har sai kin gaji. Sannan ba daga dawowarsa ne za ki fara yi masa hira ba, idan maigida ya dawo ki bashi ruwan wanka ya yi wanka sannan ki bashi abinci ya ci, kuma ya danganta da yanayinsa, wani ya fi son sai ya ci abinci kafin ya yi wanka wani kuma sai ya yi wanka sannan ya ci abinci, to ya danganta da yanayin naki maigidan, don haka yana da kyau ki sani mai yin wanka ne farko ko kuma mai cin abinci ne farko, koma dai wanne ne idan ya yi wanka ya sauke gajiyar da ya dawo da ita.
Idan mai dawowa kafin Magariba ne kafin ya yi wanka ya ci abinci lokacin magariba ya yi ya dawo ko sai bayan Sallar Isha’i kafin nan kin sake gyara kanki, idan ya dawo sai ki yi kokarin gane akwai gajiya a tare da shi ko kuma yana san a yi hira ne. Wani sai ki ga idan yana bukatar hira za ki ga ya zauna a falo to daga nan sai ki zo ki fara yi masa hira, wani yana son duk abin da ya faru a gida baya nan ki fada masa komai, to sai ki ji wani abin ma yana tambayarki, da haka sai ki ji har kun shiga wata hira can ta daban abin da ya shafe ku ne ko kuma hirar duniya ce, kuna hirarku kina dan masa tausa kina matsa masa kafafuwa daga haka idan ba ku ankara ba har sai ku ga lokaci ya tafi dare ya yi.
Idan kuma ya shiga daki to baya bukatar hira hutawa yake so ya yi sai dai ki bishi ki lallaba shi ya yi bacci.
Wani kuma sai ki ga idan kina yi masa tausa kina dan mammatsa masa kafa kina dan daddanna masa jiki sai ki ga baccin bai dauke shi ba hira ta taso.
Ya kike hirar?
Ita kanta hirar ya kamata ki san yadda za ki yi ta za muga wata idan tana magana da maigida tana yin ta gates-gatse babu tauna harshe babu ladabi kawai haka za ki ji wata macen tana watsowa mijinta magana babu wani laukwasa harshe, idan kin ga tana lankwasa harshe to a kasuwa take tana neman ragi, to ta yaya miji zai so hira da ke.
Dole ki zama mai tauna magana kafin ki furta, kuma ya kamata kisan me za ki ce ki yi tunaninta yadda idan kika fada ba za ta zamo bacin rai ba, kai wannan idan na fada ran wane zai baci to bai kamata na ce haka ba, kai ga yadda zan ce masa na san idan na fada masa wannan maganar zai ji dadinta duk a cikin ranki za ki yi wadannan maganganu kafin ki fada masa.
Kada kullum mai kawo maganganu bacin rai a’a ki rika kokarin jinye bacin ranki koda ranki a bace yake karki bari maigida ya sani.
Kin iya hirar ma kuwa wane lokaci kike zuwa hirar?
Ya kamata ku zama masu iya hira da mazajanku ku iya kalamai masu dadi ku iya hirar jan hankalin ku san maganar da ya kama ku firtawa maigida ku iya kalamai daddada masu dadi ku iya kalamai masu kwantar da hankali maigida.
Ya kamata ku san lokacin da maigida yake san hira ko kuma lokacin da ku ka ga yana cikin fara’a ko kuma ku ka ga ya sa mu hutu sosai wato ya sauke gajiya za ku iya yi masa hira a wannan lokacin.
Sannan idan maigidanki ma’aikacin gwamnati ne Asabar da Lahadi za ki ga kun fi samun lokacin hira saboda ya samu hutu, wani kuma za ki ga tun juma’a da daddare yana bukatar hira saboda ya san za’a shiga Asabar zai samu hutu.