Uwargidan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Titi Atiku Abubakar, ta bayyana cewa bai kamata ‘yan Nijeriya su yi wa mijinta Atiku Abubakar mummunan zato saboda kabilar ea ya fito.
A cewar Titi, mijin ta Bafulatani ne kuma wayayye, ba wanda ya yi rayuwar daji ba.
- Xi Jinping Ya Aikawa MDD Sakon Murnar Taron Tunawa Da Ranar Goyon Bayan Palasdinawa
- Ko Da Gaske Ne Kasar Sin Barazana Ce?
Ta bayyana hakan ne a ranar Larabar yayin gangamin yakin neman zaben jam’iyyar da aka gudanar a filin shakatawa na Dimokuradiyya a Jihar Ondo.
“Idan Atiku ya zama shugaban kasa, tabbas Nijeriya za ta fi yadda take a yanzu.
“Mun ci zaben da ya gabata, amma an tabka magudi a rumfunan zabe. Gaskiya Atiku Bafulatani ne amma ba Bafulatani daji ba ne saboda shi wayayye ne. Na kasance tare da shi sama da shekaru 40.
“A zamanin Obasanjo, Atiku ya samu makamar aikin gwamnati, ga dukkan Yarabawa Atiku na ku ne kuma shi ne zai ci zaben kasar nan.
“Lokacin da na zama matar shugaban kasa, zan kula da matasa da yara. Za a ba da tallafin karatu. Ku zabi Atiku saboda ya san makamar aiki. Akwai yunwa a kasar nan.”
A halin da ake ciki, Atiku, ya bukaci ‘yan Na
Nijeriya da kada su sake maimaita kuskuren da suka yi a 2019 a lokacin da suka zabi jam’iyyar APC mai mulki.
Atiku ya ce “Mun fara gangamin yakin neman zabenmu a Jihar Ondo a matsayin jiha ta farko a yankin Kudu maso Yamma saboda goyon bayan da kuka ba mu a 2023.
“Za mu sanya dukkan hanyoyin gwamnatin tarayya su zama masu aiki. Za mu ware isassun kudade ga matasa domin ayyukan yi. A cikin manufofinmu, mun ware dala biliyan 10 ga matasa. Dole ne mu ba su aikin yi.
“Za mu samar da kudade ga jami’o’i, ba abin da APC ta ke yi, babu mai son sake maimaita zaben APC a Nijeriya.”