Ministan ma’adanai, Dele Alake ya karbi bakuncin rukuni na farko na Askarawan kare ma’adanai da aka kafa kwanan nan domin su yi aikin kare wuraren da ake hakar ma’adanai a sassan kasar nan.
An kafa Askarawan ne a karkashin jagorancin shugaban hukumar tsaron farin kaya (NSCDC), Abubakar Audi. A ranar 1 ga watan Maris ne Ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ya kaddamar da rundunar don su yi aikin kawo karshen masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a sassan Nijeriya, wanda hakan ake sa ran zai inganta kudaden shiga a bangaren tattalin arzikin Nijeriya.
- Ba Ka Da Aiki Sai Yin Barci A Abuja – Martanin Ɗan El-Rufai Ga Uba Sani
- El-Rufai Ya Jibge Min Bashin $587 Da Biliyan 85 A Kaduna – Uba Sani
Kaddamar da dakarun ya yi daidai da bikin ranar da majalisar dinkin duniya ta ware don bikin ranar kula da hakkin fararen hula a duniya, wanda aka yi a Abuja.
Ma’aikatar ma’adanai ne ta su kula da ayyukan Askarawan.
An shirya cewa, za a tattaro dakarun ne daga jihohin tarayyar Nijeriya da babban birnin tarayya Abuja inda a halin yanzu aka kafa runduna mai mutum 60.
Alake ya umarci dakarun su tabbatar da sun kawo karshen sace-sace da ayyukan ta’addanci da ke faruwa a wuraren hakar ma’adanai a sassan Nijeriya.
Minista Alake ya kuma yaba wa Minista Olubunmi-Ojo a kan yadda ya tsayu na ganin an samu nasarar kafa rundunar.
“An kaddamar da Askarawan ne tare da hadin gwiwar ministan cikin gida don kare wuraren hakar ma’adanai, ta haka za a tabbatar da cin gajiyar albarkatun ma’adanai da Allah ya shinfida a sassan Nijeriya.Wannan kuma na daga cikin shirye-shiryen da Shugaba Tinubu ya yi na bunkasa bangaren hakar ma’adanai na Nijeriya, ”Kamar yadda Segun Tomori mai ba Minista Alake shawara a kan harkokin yada labarai ya bayyana a sanarwa da ya raba wa manema labarai.
“Ina mai farin cikin sanar da al’umma cewa, an kafa dakarun ne don tsaftace wuraren hakar ma’adanai daga matsalar tsaro, mun kuma samu nasarar kafa rukuni na farko na jami’an da za su yi wannan aikin kamar yadda muka kaddamar a yau.”