Gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar harkokin cikin gida ta biya tarar naira miliyan 585 domin a saki daurarru 4,068 da suka kasa biyan tarar da alkalai suka yanke musu a gidajen yarin Nijeriya.
Ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, wanda ya kaddamar da biyan tarar a gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja, ya ce an dauki wannan matakin ne da nufin rage cunkoso a gidajen yari da ke fadin kasar nan.
- Kasar Sin Ta Bukaci Japan Ta Amince Kasashen Duniya Su Sa Ido Kan Yadda Take Zubar Da Ruwan Dagwalon Nukiliya Cikin Teku
- Firaministan Kasar Sin Ya Gana Da Ministar Harkokin Wajen Faransa
Da yake jawabi a gidan yarin Kuje wanda aka saki fursunoni 37, Tunji-Ojo ya ce wannan sabuwar dabara ce na rage cunkoso a gidajen yarin Nijeriya.
Ya ce, “A ranar 17 ga Nuwamba, 2023, akwai kimanin fursunoni 80,804 a cikin gidajen gyaran hali da ke fadin kasar nan guda 253, wanda ya kamata a saka daurarru kasa da 50,000. Wannan ya nuna cewa akwai cunkoso a gidajen yarinmu.
“A yau, mun saki jimillar fursunoni 4,068 da ke zaman gidan yari sakamakon rashin biyan tara ko diyya.Yawancin fursunonin da suka samu ‘yancin talakawa ne da ba za su iya biyan tarar da alkalai suka yanke musu ba wanda hakan ta sa suke zaune a gidan yari.”
Ya kara da cewa kaddamar da shirin biyan naira miliyan 585 ya ta’allaka ne da kudaden da masu hannu da shuni da kungiyoyi da hukumomi suka tara wajen tallafa wa al’umma.
Tunji-Ojo ya bayyana cewa duk fursunonin da ke gidajen yari saboda rashin biyan tara ko diyya da bai wuce naira miliyan daya ba, su sukaA ci gajiyar wannan shiri. Ya kuma bayyana cewa fursunonin da aka sako an ba su jarin da za su yi wata sana’a idan suka koma yankunansu.
Tun da farko da yake jawabi, shugaban gidan yarin, Haliru Nababa, ya siffanta wannan shirin a matsayin mai matukar muhimmanci kuma abin sha’awa. Ya jaddada himma da jajircewar minista na ci gaba da sauye-sauyen da ake yi a gidajen yarin Nijeriya.
Ya kara da cewa, wannan shiri na ma’aikatar harkokin cikin gida ya samar da wani gagarumin abun yabawa ga daidaikun mutane, kamfanoni da sauran masu ruwa da tsaki.