• English
  • Business News
Thursday, July 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Minista Ya Buƙaci Sabbin Shugabannin NIPR Su Faɗakar da Jama’a Yadda Ya Dace 

by Sulaiman
7 months ago
in Labarai
0
Minista Ya Buƙaci Sabbin Shugabannin NIPR Su Faɗakar da Jama’a Yadda Ya Dace 
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya buƙaci sabbin mambobin Cibiyar Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya (NIPR) da su gudanar da harkokin sadarwa yadda ya dace da kuma bayar da gudunmawa ga cigaban ƙasa.

Ministan wanda ya samu wakilcin Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Dakta Sulaiman Haruna, ya bayyana hakan ne a wajen taron rantsar da sababbin jami’an yaɗa labarai da hulɗa da jama’a da aka gudanar a Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta Tarayya, Abuja.

  • Sanatocin Kudu Maso Gabas Sun Bukaci Duba Kudirin Dokar Gyaran Haraji
  • Netanyahu Zai Gurfana A Gaban Kotu Kan Zargin Rashawa

A nasa jawabin, Ministan ya jaddada muhimmiyar rawar da hulɗa da jama’a ke takawa wajen tabbatar da gaskiya da riƙon amana tsakanin gwamnati da ‘yan ƙasa.

Labarai Masu Nasaba

Ƴan Bindiga Sun Yi Wa Jami’an NSCDC Ƙwantan Ɓauna A Binuwe

An Kama Magungunan Jabu Na Fiye Da Naira Biliyan Ɗaya A Kano

Ya buƙaci waɗanda aka rantsar da su yi amfani da basirar su da ilimin su wajen daƙile yaɗa labaran ƙarya, inganta haɗin kai, da kuma ɗaukaka martabar Nijeriya a duniya.

“Cibiyar Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya ta daɗe tana zama ginshiƙin nagarta, tana ba da horo, ba da shaida, da kuma tsarin ɗa’a a fagen hulɗa da jama’a.

“Ta hanyar ƙoƙarin ta, NIPR ta samar da ƙwararrun masana da ke ci gaba da taka rawa wajen gina ƙasa,” inji shi.

Ya yaba wa shugabannin NIPR bisa jajircewar su wajen ciyar da wannan aiki gaba tare da jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya na samar da ingantacciyar hanyar sadarwa a matsayin ginshiƙin shugabanci na gari.

Ya ce: “A matsayi na na Mai Girma Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, na himmatu wajen tabbatar da cewa tsarin sadarwar mu na da inganci, da gaskiya, kuma sun dace da ingantattun ayyuka.

“Wannan rantsarwar ta yi daidai da babban burin mu na ƙarfafa iyawar jami’an watsa labarai a duk sassan gwamnati domin su yi hulɗa da jama’a da kuma daƙile yaɗa labaran ƙarya yadda ya kamata.”

Ministan ya buƙaci waɗanda aka rantsar ɗin da su kiyaye ƙwarewa da riƙon amana, musamman a zamanin gidan yana, inda ya bayyana rawar da suke takawa a matsayin mai muhimmanci ga haɗin kan ƙasa da kuma bunƙasa al’adun gargajiyar Nijeriya.

“Ga sababbin membobin da aka rantsar, yau ne farkon wani sabon babi a tafiyar ku ta aiki.

“Aikin ku ba wai kawai yana nuna yadda ƙungiyarku ko cibiyar ku yake ba; yana nuni ga ɗaukacin al’ummar ƙasar. Ku kiyaye ƙa’idojin NIPR kuma ku kasance jakadun gaskiya da nagarta,” inji shi.

Da yake jawabi a wurin taron, Shugaban Cibiyar Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya (NIPR), Dakta Ike Neliaku, ya bayyana jin daɗin sa da shigar da sabbin mambobi cikin cibiyar.

Shugaban ya jaddada muhimmancin aikin hulɗa da jama’a, inda ya ce, “Ba sa’a kawai kuka yi ba, haƙiƙa kun samu albarka, domin a yanzu kun shiga cikin aikin fitattun mutane, aiki ɗaya tilo da ba ya tsufa, aiki ɗaya tilo da ke mu ku jagorar samun abubuwa mafi kyawu daga rayuwa.”

Shugaban ya miƙa godiyar sa ga Ministan Yaɗa Labarai bisa rawar da ya taka wajen inganta harkar hulɗa da jama’a.

Ya bayyana ƙoƙarin da Ministan ya yi wajen ganin an amince da hulɗa da jama’a a matsayin aiki a aikin gwamnati.

“A shekarar da ta gabata, ya ɗauki nauyin rubutawa majalisa ta 45 kan kafawar a Bauchi, kuma a ranar 13 ga Disamba, 2023, majalisar ta yi la’akari da wannan takardar kuma ta amince da shi,” inji shugaban.

“Wannan wani muhimmin cigaba ne ga aikin mu, saboda yana nuna mahimmancin sadarwa mai inganci a cikin shugabanci.”

Ya nanata muhimmancin jami’an hulɗa da jama’a wajen samar da amana da fahimtar juna tsakanin gwamnati da jama’a.

“Idan aka yi hulɗa da jama’a yadda ya kamata, za su mallaki shirye-shiryen gwamnati. Idan aka yi hulɗa da jama’a yadda ya kamata, suna ba da shawarar abin da ya kamata a yi. Idan aka bai wa ‘yan kasa damar bayyana ra’ayoyinsu, yana da matuƙar amfani wajen samar da daidaito,” inji shi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Xi Jinping Ya Gana Da Manyan Jami’An Muhimman Kungiyoyin Tattalin Arziki Na Kasa Da Kasa

Next Post

Yaki Da Talauci: Yadda Kasar Sin Ke Taka Rawar Gani A Duniya 

Related

Ƴan Bindiga Sun Yi Wa Jami’an NSCDC Ƙwantan Ɓauna A Binuwe
Manyan Labarai

Ƴan Bindiga Sun Yi Wa Jami’an NSCDC Ƙwantan Ɓauna A Binuwe

2 hours ago
An Kama Magungunan Jabu Na Fiye Da Naira Biliyan Ɗaya A Kano
Labarai

An Kama Magungunan Jabu Na Fiye Da Naira Biliyan Ɗaya A Kano

3 hours ago
Majalisar Ta Kwace Shugabacin Kwamitin Da Natasha Ke Jagoranta
Labarai

Majalisar Ta Kwace Shugabacin Kwamitin Da Natasha Ke Jagoranta

5 hours ago
Shiri Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Tabbatar Da Ci Gaban Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Shiri Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Tabbatar Da Ci Gaban Kasar Sin

5 hours ago
EFCC Ta Gargaɗi Ƴan Nijeriya Kan Ɓullar Sabbin Hanyoyin Damfarar Kuɗi
Labarai

EFCC Ta Gargaɗi Ƴan Nijeriya Kan Ɓullar Sabbin Hanyoyin Damfarar Kuɗi

6 hours ago
Dangote Ya Yaba Wa Tinubu Kan Samar Da Ababen More Rayuwa A Nijeriya
Labarai

Dangote Ya Yaba Wa Tinubu Kan Samar Da Ababen More Rayuwa A Nijeriya

9 hours ago
Next Post
Yaki Da Talauci: Yadda Kasar Sin Ke Taka Rawar Gani A Duniya 

Yaki Da Talauci: Yadda Kasar Sin Ke Taka Rawar Gani A Duniya 

LABARAI MASU NASABA

Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Kai Matakin Kwata Fainal Bayan Doke Botswana

Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Kai Matakin Kwata Fainal Bayan Doke Botswana

July 10, 2025
Mataimakin Babban Magatakardan MDD: Sin Aminiya Ce Da Afirka Za Ta Iya Dogaro Da Ita

Mataimakin Babban Magatakardan MDD: Sin Aminiya Ce Da Afirka Za Ta Iya Dogaro Da Ita

July 10, 2025
Li Qiang Ya Gana Da Manyan Jami’an Masar Da ALLi Qiang Ya Gana Da Manyan Jami’an Masar Da AL

Li Qiang Ya Gana Da Manyan Jami’an Masar Da ALLi Qiang Ya Gana Da Manyan Jami’an Masar Da AL

July 10, 2025
Ƴan Bindiga Sun Yi Wa Jami’an NSCDC Ƙwantan Ɓauna A Binuwe

Ƴan Bindiga Sun Yi Wa Jami’an NSCDC Ƙwantan Ɓauna A Binuwe

July 10, 2025
Yadda JKS Ta Jure Tsawon Tarihin Gwagwarmaya Da Cimma Nasarori

Yadda JKS Ta Jure Tsawon Tarihin Gwagwarmaya Da Cimma Nasarori

July 10, 2025
An Kama Magungunan Jabu Na Fiye Da Naira Biliyan Ɗaya A Kano

An Kama Magungunan Jabu Na Fiye Da Naira Biliyan Ɗaya A Kano

July 10, 2025
Xi Jinping Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Bude Taron Ministocin Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Wayewar Kan Bil Adam

Xi Jinping Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Bude Taron Ministocin Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Wayewar Kan Bil Adam

July 10, 2025
Majalisar Ta Kwace Shugabacin Kwamitin Da Natasha Ke Jagoranta

Majalisar Ta Kwace Shugabacin Kwamitin Da Natasha Ke Jagoranta

July 10, 2025
An Bude Taron Ministoci Kan Wayewar Kai A Birnin Beijing

An Bude Taron Ministoci Kan Wayewar Kai A Birnin Beijing

July 10, 2025
Shiri Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Tabbatar Da Ci Gaban Kasar Sin

Shiri Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Tabbatar Da Ci Gaban Kasar Sin

July 10, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.