Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya roƙi kamfanin taskace bayanai a intanet (Google), da ya daƙile bazuwar dukkan saƙwannin da ka iya zama haɗari da barazana ga ɗorewar dunƙulalliyar al’umma a ƙasa ɗaya.
Ministan ya yi wannan kira ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar manyan jami’an Google na Afrika ta Yamma, bisa jagorancin daraktansu, Mista Olumide Balogun.
- CMG Ya Kaddamar Da Bikin Baje Kolin “Hanyar Samun Wayewar Kai” A London
- ‘Yan Nijeriya Za Su Iya Tara Min Kudi Don Yi Wa Tinubu Waka Saboda Kaunarsa -Mawaki Rarara
Tawagar ta kai masa ziyara ne a ranar Alhamis, a Abuja.
Ya ce: “Akwai matuƙar muhimmanci a ga cewa an tantance tasiri da kuma illolin manhajojin yaɗa bayanai ta intanet. Ina ganin ku ne aikin hana yaɗuwar abu mai illa ya fi wajaba a kan ku.
“Gwamnati ba ta da aniya ko tunanin ƙaƙaba wa ‘yancin faɗar albarkacin baki ko ‘yan jarida takunkumi. Shugaban Ƙasa ba mai so ya ga ana tauye ‘yancin faɗar albarkacin baki ba ne.
“To sai dai kuma, idan har aka ce bayani mai haɗari ne, zai iya zama babbar matsala kenan a gare mu. Zai tarwatsa haɗin kanmu tare da haifar mana da ruɗu a cikin ƙasa.
“Mun san cewa isar da saƙwannin bayanai ta intanet na da muhimmanci sosai wajen ɗorewar ƙasa har ta tsaya da diddiginta a matsayin ƙasa. Don haka akwai buƙatar samun ‘yancin bayyana ra’ayi a kafar da kowa zai ji ba a tauye masa haƙƙi ko ‘yanci ba.
“Saboda haka, muddin aka samu fahimta ta hanyar isar da sakonnin bayanai a cikin jama’a, to za a rage ɗarɗar da ambaliyar labarai na bogi. A kula, ‘yanci ya na tafiya ne tare da sanin ƙa’idoji da ya kamata.”
Minista ya ƙara da cewa, Google na da gagarumin haƙƙi na ganin cewa haƙƙin da aka bai wa mutane su na watsa bayanai a kafafen sada zumunta bai zama musabbabin haifar da hargitsi ga ‘yan Nijeriya ba.
Da ya ke nasa jawabin tun da farko, Mista Balogun ya shaida wa ministan cewa, cikin shekaru uku da su ka gabata zuwa yanzu kamfanin ya horas da ‘yan jarida 3,500 a Nijeriya.
Ya ce an horas da su ne dabarun amfani da hanyoyin fasahar zamani wajen tantance sahihan labarai, da tace labaran bogi da sauran su.