• English
  • Business News
Sunday, October 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Minista Ya Yaba Wa Hafsoshin Soji Kan Cigaban Da Aka Samu A Fannin Tsaron Ƙasa

by Sulaiman
4 months ago
Minista

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yaba wa Hafsoshin Sojin ƙasar nan bisa kyakkyawan sauyin da aka samu a fannin gudanar da aikin tsaro cikin shekaru biyu da suka gabata, wanda ya haifar da gagarumin cigaba da ba ya misaltuwa a fannin tsaron ƙasa baki ɗaya.

 

Mataimaki na Musamman ga ministan kan harkokin yaɗa labarai, Malam Rabi’u Ibrahim, ya ruwaito a cikin sanarwar da ya rattaba wa hannu cewa Idris ya yi wannan kalamin ne a ranar Alhamis, yayin wani taron tattaunawa da manyan shugabannin kafafen yaɗa labarai da sauran masu ruwa da tsaki, wanda aka gudanar a Hedikwatar Tsaro da ke Abuja, domin bikin cika shekaru biyu da naɗa Hafsoshin Soji da ke kan karaga yanzu.

  • Hajjin Bana: Jihohi 11 Sun Kashe Naira Biliyan 6.2 Kan Mahajjata
  • Sin Ta Jadadda Wajibcin Daukar Jerin Matakan Magance Matsalar Talauci Da Karancin Ci Gaba Da Rikici

Ministan ya ce: “Bari in fara da isar da jinjina daga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu (GCFR) ga Hafsoshin Sojin mu kan jajircewar su babu ƙaƙƙautawa, da ɗa’ar su da ƙaunar ƙasa wajen sauke nauyin da ke kan su.”

 

LABARAI MASU NASABA

Ɗan Majalisa Ya Ce Ba Zai Sake Takara Ba, Ya Sadaukar Da Ita Ga Matasa

Abin Da Ya Sa Aka Yi Watsi Da Tashar Jiragen Ruwa Ta Kan Tudu Da Ke Jihar Kaduna

Idris, wanda shi ne ya jagoranci zaman, ya bayyana irin nasarorin da aka samu a ƙarƙashin jagorancin Babban Hafsan Tsaro da sauran Hafsoshin Sojin a matsayin mai tabbataccen tasiri da gamsasshen sakamako.

 

Ya ce: “Abin da muka gani ba wai kawai daƙile waɗannan barazanar ba ne, sai dai ma sake karɓe sararin ƙasar mu, da tunanin jama’a, da kuma a matakin aiki. Yanzu ‘yan Nijeriya za su iya tabbatar da cewa manyan hanyoyin mu sun fi samun tsaro ƙwarai idan aka kwatanta da ‘yan shekarun baya.”

 

Ya lissafa nasarorin da rundunonin sojin Nijeriya suka samu a sassa daban-daban na ƙasar nan, ciki har da yankin Arewa-maso-gabas da gaɓar teku.

Minista

“Daga nasarar ragargaza sansanonin Boko Haram da ISWAP a Arewa-maso-Gabas, zuwa irin gagarumin farmakin da aka kai kan maɓoyar ‘yan bindiga a Arewa-maso-Yamma da Arewa-ta-Tsakiya; daga ingantaccen sintirin da sojin ruwa ke yi wanda ya rage yawan satar ɗanyen mai da rushe haramtattun matatun mai; zuwa luguden wutar sama da ba ya ƙarewa wanda ya tarwatsa hanyoyin sufuri da ɗaukar kaya na miyagun mutane — sakamakon da aka samu ba kawai abin burgewa ba ne, har ma abin kwantar da hankali ne.”

 

Ministan ya kuma jaddada muhimmancin rawar da kafafen yaɗa labarai suke takawa wajen gina ƙasa, yana mai roƙon su da su tallafa wa ƙoƙarin da rundunonin tsaro suke yi ta hanyar yaɗa nasarorin da suke samu.

 

Ya ce: “Ya kamata kafafen yaɗa labarai su riƙa bada rahoto ba kawai kan abin da ya zama ba daidai ba, har ma da abin da ake yi daidai. Ku riƙa hasko irin sadaukarwar da dakarun mu suke yi. Ku bada labaran cigaba da ake samu. Ku daidaita suka da cikakken bayani. Wannan shi ne ainihin aikin jarida bisa ƙwarewa.”

 

Ya bada tabbacin cewa gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da tallafa wa rundunar soji ba kawai da kayan aiki kaɗai ba har ma da tsare-tsaren dabarun da za su inganta tattara bayanan sirri, haɗin gwiwar hukumomi, da walwalar ma’aikata.

 

Ya yaba wa Hafsoshin Sojin bisa shugabancin su na kishin ƙasa da samar da sakamako mai tasiri.

 

“Kun dawo da fata, kun ceci rayuka, kun kare martabar ƙasar mu, kuma fiye da komai ma, kun tunatar da mu ma’anar yi wa ƙasa hidima,” inji shi.

 

Ya kuma buƙaci kafafen watsa labarai da sauran masu ruwa da tsaki da su riƙa haska irin nasarorin da ake samu, yana mai cewa hakan yana da matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa gwiwar jami’an tsaro.

 

“Ku lura da cigaban da ake samu kuma ku faɗaɗa yaɗuwar sa. Wannan na da matuƙar amfani ga ɗimbin dakarun mu da ke aiki dare da rana don kare ƙasar nan da samar da yanayin da duk ‘yan Nijeriya za su iya rayuwa, su yi aiki, su bunƙasa.”

 

Taron ya samu halartar Ministan Tsaro, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, wanda Manjo Janar A.T. Jibrin (ritaya) ya wakilta; da Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa; da Manajan Daraktan Kamfanin Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN), Malam Ali M. Ali; da Babban Daraktan Hukumar Gidajen Rediyon Nijeriya (FRCN), Dakta Mohammed Bulama; da Babban Daraktan Muryar Nijeriya (VON), Malam Jibrin Baba Ndace; da Shugaban da Shugaban Majalisar Ƙungiyar Masana Harkokin Yaɗa Labarai ta Nijeriya (NIPR), Dakta Ike Neliaku; da wakilan Hafsoshin Soji, da manyan shugabannin kafafen yaɗa labarai.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ɗan Majalisa Ya Ce Ba Zai Sake Takara Ba, Ya Sadaukar Da Ita Ga Matasa
Labarai

Ɗan Majalisa Ya Ce Ba Zai Sake Takara Ba, Ya Sadaukar Da Ita Ga Matasa

October 26, 2025
Abin Da Ya Sa Aka Yi Watsi Da Tashar Jiragen Ruwa Ta Kan Tudu Da Ke Jihar Kaduna
Labarai

Abin Da Ya Sa Aka Yi Watsi Da Tashar Jiragen Ruwa Ta Kan Tudu Da Ke Jihar Kaduna

October 26, 2025
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi
Labarai

‘Yansanda Sun Kama Wasu Mutum Biyu Da Ake Zargi Da Haɗa Baki Da ‘Yan Bindiga A Kano

October 26, 2025
Next Post
Ƴansanda Sun Gargaɗi Masu Lalata Fastar Tinubu A Kano

Ƴansanda Sun Gargaɗi Masu Lalata Fastar Tinubu A Kano

LABARAI MASU NASABA

Ɗan Majalisa Ya Ce Ba Zai Sake Takara Ba, Ya Sadaukar Da Ita Ga Matasa

Ɗan Majalisa Ya Ce Ba Zai Sake Takara Ba, Ya Sadaukar Da Ita Ga Matasa

October 26, 2025
Abin Da Ya Sa Aka Yi Watsi Da Tashar Jiragen Ruwa Ta Kan Tudu Da Ke Jihar Kaduna

Abin Da Ya Sa Aka Yi Watsi Da Tashar Jiragen Ruwa Ta Kan Tudu Da Ke Jihar Kaduna

October 26, 2025
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

‘Yansanda Sun Kama Wasu Mutum Biyu Da Ake Zargi Da Haɗa Baki Da ‘Yan Bindiga A Kano

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwamnatin Kaduna Tare Da  AUDA–NEPAD Sun Tallafa Wa Manoma 400 Da Kayan Noma

October 26, 2025
Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

October 26, 2025
Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ɗan Majalisa Na Shekarar 2025: Benjamin Okezie Kalu

October 26, 2025
An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 25, 2025

Nafisa Abdullahi Aminu: Yarinyar Da Ta Ɗaukaka Darajar Nijeriya A Idon Duniya

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.