• English
  • Business News
Monday, October 20, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ministan Ayyuka Ya Jinjina Wa Gwamnan Zamfara Kan Ayyukan Sabunta Birane

by Leadership Hausa
2 years ago
zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya samu yabo daga Ministan Ayyuka, David Umahi, bisa gagarumin ci gaban da gwamnatinsa ta samu a ayyukan sabunta birane.

A ranar Juma’ar ce Ministan ya kai ziyarar aiki Jihar Zamfara a wani rangadin da yake yi na duba ayyukan titunan Gwamnatin Tarayya a jihar.

Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta ce ministan ya duba ayyukan titunan Gwamnatin Tarayya da ke gudana wanda ya kai tsawon kilomita 277.305, daga Zariya zuwa Sheme, Sheme zuwa Gusau, da Gusau zuwa Mafara.

Sanarwar ta ƙara da cewa, ministan da muƙarrabansa sun lura da ɗumbin nasarorin da aka samu a aikin sabunta biranen da gwamnatin Gwamna Lawal ke gudanarwa.

  • Yadda Gwamnati Ke Kara Shan Matsin Lamba A Kan Yunwa

LABARAI MASU NASABA

Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC

Ɗan Jarida Ibrahim Ɗan’uwa Rano Ya Shaƙi Iskar Ƴanci Bayan Tsare Shi

A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya yaba wa ministan bisa yunƙurinsa na duba ayyukan manyan titunan Gwamnatin Tarayya.

“Ina tabbatar muku da cewa akwai alheri domin akan bayar da kwangilar gina tituna, amma babu wanda ke zuwa dubawa daga Gwamnatin Tarayya. Zuwar ku na da matuƙar amfani..

“Minista, kamar yadda ka tabbatar, ba a daina faɗaɗa hanyoyi ba, kamar yadda ake ta yayatawa. Wannan labari ne mai daɗi.

“Ina so in nuna godiyata da kyawawan kalamanka. A matsayinmu na gwamnati mai kishin ƙasa, muna aiki tuƙuru don ganin mun canja mummunan yanayin Jihar Zamfara. A da, duk lokacin da ka ji labarin Jihar Zamfara, a kan yi tunanin abu mara kyau ne. Amma yanzu muna ƙoƙarin ceto da sake gina jihar.

“Ina kuma son in yi godiya ga shugaban ƙasa bisa ga ƙoƙarin da ya yi na aiwatar da muhimman ayyukan Gwamnatin Tarayya. Za mu ci gaba da goyon bayan kyawawan manufofinsa.”

A jawabinsa, ministan ayyuka, David Umahi, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne umarci a yi rangaɗin domin ganin yadda ayyukan ke gudana.

“Gwamna, mun zo nan ne bisa umarnin shugaban ƙasa domin duba ayyukan tituna da ke gudana tare da isar da gaisuwarsa gare ku.

“Shugaban ƙasa ya ƙuduri aniyar kammala dukkan ayyukan da ake gudanarwa, da suka haɗa da faɗaɗa titunan tarayya, ba a Zamfara kaɗai ba har ma a faɗin ƙasar nan baki ɗaya.

“Ina yaba muku kan ƙoƙorin ku na ci gaba da aiwatar da ayyukan sabunta birane da suka kawo sauyi a Zamfara cikin watanni tara kacal.”

Shugaban kwamitin Majalisar Dattijai mai kula da gidaje da tituna, Aminu Waziri Tambuwal, tsohon gwamnan Jihar Sakkwato yana cikin tawagar ministan.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC
Labarai

Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC

October 19, 2025
Ɗan Jarida Ibrahim Ɗan’uwa Rano Ya Shaƙi Iskar Ƴanci Bayan Tsare Shi
Manyan Labarai

Ɗan Jarida Ibrahim Ɗan’uwa Rano Ya Shaƙi Iskar Ƴanci Bayan Tsare Shi

October 19, 2025
Ƴansanda Sun Kama Ɗan Jarida A Kano Bisa Zargin Ɓata Suna
Manyan Labarai

Ƴansanda Sun Kama Ɗan Jarida A Kano Bisa Zargin Ɓata Suna

October 19, 2025
Next Post
Buhari Ya Haddasa Wa Nijeriya Koma-baya Na Tsawon Shekara 50 — Fayose

Buhari Ya Haddasa Wa Nijeriya Koma-baya Na Tsawon Shekara 50 — Fayose

LABARAI MASU NASABA

Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A Karon Farko A Tarihin Gamuwarsu

Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A Karon Farko A Tarihin Gamuwarsu

October 19, 2025
Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20

Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20

October 19, 2025
Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC

Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC

October 19, 2025
Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin

Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin

October 19, 2025
Ɗan Jarida Ibrahim Ɗan’uwa Rano Ya Shaƙi Iskar Ƴanci Bayan Tsare Shi

Ɗan Jarida Ibrahim Ɗan’uwa Rano Ya Shaƙi Iskar Ƴanci Bayan Tsare Shi

October 19, 2025
Tie Ning Ta Halarci Bikin Bude Taron Karawa Juna Sani Na ‘Yan Majalisun Dokokin Kasashen Afirka

Tie Ning Ta Halarci Bikin Bude Taron Karawa Juna Sani Na ‘Yan Majalisun Dokokin Kasashen Afirka

October 19, 2025
Ƴansanda Sun Kama Ɗan Jarida A Kano Bisa Zargin Ɓata Suna

Ƴansanda Sun Kama Ɗan Jarida A Kano Bisa Zargin Ɓata Suna

October 19, 2025
Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Kuma Illolin Rashin Yawan Sha

Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Kuma Illolin Rashin Yawan Sha

October 19, 2025
Xinjiang Ta Janyo Karin Jari A Rubu’i Uku Na Farkon Shekarar Nan

Xinjiang Ta Janyo Karin Jari A Rubu’i Uku Na Farkon Shekarar Nan

October 19, 2025
Yadda Shagwaɓa Kananan Yara Da Kudi Ke Shafar Tarbiyyarsu

Yadda Shagwaɓa Kananan Yara Da Kudi Ke Shafar Tarbiyyarsu

October 19, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.