Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da sakatare janar na MDD Antonio Guterres, a gefen babban taron MDD na 77 a ranar 23 ga wata.
Yayin ganawar, Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin ta dade tana kira ga manyan kasashe, musammam masu kujerar dindindin a kwamitin sulhu na majalisar, da su zama ja gaba wajen kiyaye dokokin kasa da kasa da tabbatar da ikon MDD, da inganta tsarin huldar kasa da kasa a aikace, tare da taimakawa kasashe masu tasowa.
Ya kara da cewa, abun takaici ne yadda wasu manyan kasashe ke ware kansu, sannan su kira shi da huldar kasa da kasa domin wata moriyarsu ta kashin kai, da kuma fakewa da bin doka yayin da suke kafa wasu kananan rukunoni a ko ina.
Har ila yau, Wang Yi ya ce, kasar Sin na goyon bayan MDD, haka kuma tana goyon bayan matsayinta na jagorantar al’amuran duniya, tare da marawa majalisar baya wajen kara taka rawa domin shawo kan kalubalen da tsaro da zaman lafiya.
A nasa bangaren, Antonio Guterres ya yaba da muhimmiyar rawar da Sin ta dade tana takawa wajen daukaka huldar kasa da kasa da hadin gwiwarsu da ci gaba mai dorewa, yana mai cewa, huldar majalisar da kasar Sin, muhimmin tubali ne ga majalisar da tsarin huldar kasa da kasa.
Ya ce bangarorin biyu na hadin gwiwa ta kut da kut, kuma MDD na goyon bayan shawarar raya duniya ta GDI da shugaban Sin ya gabatar. (Fa’iza Mustapha)