Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya halarci taron ministocin kungiyar BRICS a jiya Litinin a birnin Nizhni Novgorod na kasar Rasha.
Yayin taron, Wang Yi ya ce, hadin gwiwar kasashen BRICS ya gudana cikin sauri da inganci a cikin shekara daya da ta gabata, inda har BRICS ta shigar da sabbin mambobi, matakin da ya bude sabon babin hadin gwiwar kasashe masu tasowa dake dogaro da karfinsu, abin da ya sa BRICS ke kara jan hankalin duniya.
- Xi Ya Jaddada Muhimmancin Inganta Tsarin Kamfanoni Na Zamani Mai Halayyar Musamman Ta Sin
- Kasar Sin Ta Gada Tare Da Raya Al’Adun Da Suka Shafi Bikin Gargajiya Na Duanwu
Wang Yi ya ce, “dole ne mu nace ga tabbatar da adalci da gaskiya, mu bi hanyar da ta dace da yanke shawara yadda ya kamata, duba da cewa ana fuskantar ja-in-ja tsakanin ra’ayin mu’amalar bangarori daban daban a duniya da na babakere, da ma ra’ayin bangarori da na kashin kai.”
Ya kara da cewa ya kamata a yi amfani da tsare-tsare da tasirin siyasar kungiyar yadda ya kamata don mai da BRICS wani sabon tsari mai yakini na hadin kan kasa da kasa da bude kofa dake dogaro da tushen kasuwanni masu saurin ci gaba da karfin kasashe masu tasowa.
Mahalarta taron sun yabawa babban tasiri da ci gaban shigar da sabbin mambobi da BRICS ya samu, inda suke ganin cewa, shigar da karin mambobi cikin kungiyar za ta gaggauta samar da iko tsakanin bangarori da dama a duniya da ingiza doka da odar kasa da kasa mai adalci da daidaito, kuma sun amince da tsarin shigar da kasashen hulda cikin kungiyar, inda kuma aka gabatar da “Hadaddiyar Sanarwa Game Da Ganawar Ministocin Wajen Kasashen BRICS”.
Sannan a yayin taron, Wang Yi ya gana da takwaransa na Habasha, Taye Atske Selassie, a birnin Nizhny Novgorod na kasar Rasha.
Da yake bayyana Habasha a matsayin muhimmiyar kasa a nahiyar Afrika, kuma mai masaukin hedkwatar kungiyar Tarayyar Afrika (AU), Wang Yi ya ce, zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasar na da muhimmanci ga nahiyar. Ya kara da cewa, a shirye Sin take ta zurfafa abota cikin kowanne yanayi, da fadada hadin gwiwa a bangarori daban daban, da kuma ingiza samun karin nasarori a dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, domin jama’arsu su amfana da su.
A nasa bangare, Taye Atske Selassie ya ce, gwamnati da al’ummar Habasha na maraba da daukaka dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa ta abota bisa manyan tsare-tsare a kowanne yanayi. Ya kara da cewa, kasar Sin ce babbar mai zuba jari a Habasha, haka kuma inda ta fi shigar da kayayyakinta, kana dangantakar dake tsakaninsu ta bunkasa tattalin arziki da kyautata zamantakewar Habasha.
Bugu da kari, Wang Yi ya gana da takwaransa ta Afirka ta kudu Naledi Pandor, a garin Nizhni Novgorod na kasar Rasha.
Yayin zantawar tasu a jiya Talata, Wang Yi ya taya Afirka ta kudu murnar gudanar da babban zaben kasa cikin nasara. Yana mai bayyana yadda Sin ke dora muhimmancin gaske ga ci gaban Afirka ta kudu, a matsayin ta na babbar kasa mai tasowa. Ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tukuru tare da sassan kasa da kasa a fannin tsare tsare, da samar da murya mai ma’ana, kuma mai daidaito, game da muhimman batutuwa dake addabar duniya, kamar rikicin Ukraine, kana tana fatan ba da gudummawa ga wanzar da zaman lafiya da daidaito a duniya.
A nata bangare kuwa, Naledi Pandor, cewa ta yi Afirka ta kudu na jinjinawa kokarin kasar Sin, na ganin an warware rikicin Ukraine ta hanyar siyasa, da yayata bukatar dakatar da bude wuta a Gaza. Ta ce Afirka ta kudu a shirye take ta karfafa hadin gwiwa da Sin, karkashin dandalolin kasa da kasa, irin su kungiyar BRICS, da G20, don tabbatar da an cimma nasarar raya ci gaban tsare tsaren da ake gudanarwa karkashin su yadda ya kamata. (Masu Fassarawa: Saminu Alhassam, Fa’iza Mustapha, Amina Xu)