A yau Talata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi alkawarin dora kasar Sin a kan turbar zama wani kakkarfan ginshiki na wanzar da zaman lafiya, da hadin kai, da bude kofa, da adalci da kuma hadaka a duniya. Ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a taron tattaunawa game da manufofin ketare a birnin Beijing.
A taron tattaunawar game da halin da ake ciki a kasashen duniya da kuma manufofin hulda da waje na kasar Sin a shekarar 2024, Wang Yi, wanda har ila yau mamba ne a hukumar siyasa ta kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ya kara da cewa, gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai-daya ga dan Adam ya kasance babban burin kasar Sin ta fuskar gudanar da salon huldarta ta diflomasiyya da kasashen duniya.
- Xi Jinping: Ana Kokarin Raya Tsibirin Hainan Bisa Zamanintarwa Irin Na Kasar Sin
- Sin Ta Bayyana Matukar Adawa Da Aniyar Amurka Ta Sanya Karin Haraji Kan Wasu Hajojin Sin Dake Shiga Kasar
Ya ce, game da batun rikicin Ukrain, kasar Sin ta yi tsayuwar daka a tsakiya ba tare da nuna goyon bayan bangare guda ba, tare da bayar da shawarwari a kan dawo da zaman lafiya da hawa teburin tattaunawa.
Da ya juya ga batun Gaza kuwa, Wang ya ce babban abin da aka fi bukata cikin gaggawa shi ne cikakkiyar tsagaita wuta da kawo karshen muzgunawar da ake yi a zirin Gaza, kuma muhimmin abin da aka fi mayar da hankali a kai shi ne tabbatar da kai kayan agaji, kana tushen warware rikicin na hakika shi ne tabbatar da kafa kasashe biyu a yankin.
Wang Yi ya yi kira ga gwamnatin Amurka mai jiran gado ta dauki matakan da suka dace, da yin aiki tare da kasar Sin bisa alkibla daya, da daina tsoma baki, da kawar da kawo cikas tare da mikewa haikan ga inganta alakar Sin da Amurka mai dorewa ba tare da tangarda ba.
Hakazalika, Wang ya ce, kasar Sin za ta kara zurfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni da kasar Rasha da karfafa alakarta da Tarayyar Turai don samun ci gaba a bisa tafarki mai ’yanci, da cin gajiyar juna da kuma cin moriyar duniya baki daya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)