Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana ta kafar bidiyo, da jakadun wasu kasashe masu tasowa na Asia da Afrika dake ofishin MDD dake Geneva, wadanda suke ziyara a kasar Sin bisa gayyatar da bangaren kasar Sin ya yi musu.
Yayin ganawar ta jiya, Wang Yi ya ce a shirye kasar Sin take, ta daukaka burin gina alumma mai makoma ta bai daya ga bil adama, da hada hannu da sauran kasashe masu tasowa wajen samun ci gaba da kwanciyar hankali da kuma kara kyautata duniya.
Ya kuma yi bayani game da asalin batun Taiwan da matsayar kasar Sin. Yana mai jaddada cewa, wajibi ne kasar Sin ta dauki dukkan matakan da suka dace kuma suka halatta, ga duk wata takalar Amurka.
A nasu bangaren, jakadun sun yabawa manyan nasarorin da Sin ta samu da karfin shugabancinta, da kuma kokarinta na inganta ci gaba da daidaito tsakanin alumma.
Sun kara da cewa, manufar Sin daya tak a duniya da kuduri mai lamba 2758 na babban zauren MDD ya amince da shi, matsaya ce ta daukacin kasashen duniya, kuma kaidar huldar diflomasiyya tsakanin Sin da dukkan kasashe.
Sun kara da cewa, yankunan Taiwan da Xinjiang, bangarori ne na kasar, kuma harkokin cikin gidan kasar Sin ba sa bukatar katsalandan daga waje. (Mai Fassarawa: Faiza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp