Ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang, zai gabatar da jawabi ta kafar bidiyo ga taron manyan jami’ai na zama 52 na majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD.
Da take tsokaci, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning, ta bayyana cewa, kasar Sin na bin hanyar da ta zabarwa kanta, ta inganta batutuwan da suka shafi kare hakkin dan adam, da shiga ana damawa da ita wajen tafiyar da batutuwa masu ruwa da tsaki a duniya, haka kuma ta cimma nasarori a kokarinta na kare hakkokin jama’a.
Ta kara da cewa, yunkurin kare hakkin dan adam a duniya na fuskantar kalubale a yanzu, lamarin dake bukatar dukkan bangarori su gaggauta cimma matsaya da karfafa hadin gwiwa.
An fara zama na 52 na majalisar kare hakkin dan adam ta MDD, yau Litinin a ofishin MDD dake Geneva, inda sakatare janar na majalisar Antonio Guteress, ya gabatar da jawabin bude zaman.
A cewar kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning, zaman na 52 na majalisar, zai fara ne daga yau 27 ga wata zuwa 4 ga watan Afrilu, yayin da zaman manyan jami’ai zai gudana daga yau 27 zuwa 2 ga watan Maris.(Lubabatu)