Ministan noma na kasar Gambiya Demba Sabally ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a kwanan baya cewa, goyon baya da taimakon fasaha na kasar Sin sun taka muhimmiyar rawa wajen samar da gagarumin ci gaba a fannin aikin gona na Gambiya a shekarun baya-bayan nan.
Ministan ya ce, yawan amfanin gona da kasar ta Gambiya ke samu na ci gaba da karuwa, inda yawan shinkafar da kasar ta samar ya haura tan 48,000 a shekarar 2024, wanda ya kafa tarihi. Sabally ya kuma bayyana cewa, kirkire-kirkire a fannin samar da ababen more rayuwa, da fasahohin aikin gona masu yawan gaske da tawagogin kasar Sin suka yi amfani da su, sun taka rawa wajen kai wa ga wannan matsayi.
- Halayen Kirki 14 Da Ake Bukata Daga Malamin Makaranta (3)
- Nijeriyar Jiya Da Yau: Kiki-Kakar Sabgar ‘Yan Majalisu
Yana mai cewa, tawagar kwararrun kasar Sin sun ba da taimako a kasar Gambiya ta hanyar gabatar da nau’o’in shinkafa masu inganci da suka hada da ire-iren da aka tagwaita da masu samar da girbi mai yawa, wadanda ke da matukar muhimmanci ga bunkasa aikin gonar Gambiya.
Sabally ya kammala da cewa, Gambiya za ta ci gaba da tura ma’aikatan aikin gona zuwa kasar Sin don samun horo mai zurfi, kuma yana fatan zurfafa hadin gwiwa a tsakanin kasarsa da Sin a fannin aikin gona, da sabbin fasahohi, da bunkasa hazaka. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp