Ministan kula da sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika, ya sanar da wanda zai maye kujerar Manajan Gudanarwa (MD) na hukumar kula da filayen jiragen kasar nan (FAAN), yayin da wa’adin aikin Kaftin Rabiu Yadudu ya kare.
Sirika ya maye gurbin Yadudu ne da Kabir Yusuf Mohammed bayan da wa’adin shugabancin a hukumar FAAN ya kare a ranar Asabar 20 ga watan Mayun 2023.
- FAAN Ta Bai Wa Kamfanonin Jirage Umarnin Kwashe Jiragensu Daga Filin Jirgin Saman Abuja
- Matar Farfesa Yadudu Ta Rasu A Kasar AmurkaÂ
LEADERSHIP ta labarto cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Kaftin Yadudu ne a matsayin MD na FAAN a ranar 20 ga watan Mayun 2019.
Da ya ke zantawa da LEADERSHIP, babban Sakataren ARTI, Kaftin John Ojikutu (Mai ritaya) ya ce tuni aka maye gurbin kujerar Yadudu.
Koda yake duk kokarin da LEADERSHIP ta yi don jin ta bakin hukumomi kan nadin abun ya ci tura, duk da sakonnin da muka aike wa Kakakin FAAN, Faithful Hope-Ivbaze, amma ba amsa har zuwa hada wannan rahoton.
Kafin a masa nadi a matsayin sabon MD, Kabir Mohammed shi ne Manajan shiyya na hukumar da ke kula da shiyyar Arewa ta Tsakiya.
Nadin ya zo da ban mamaki matuka kura da cewa shi kansa ministan kwanaki kadan ne suka rage masa ya bar ofishinsa.
Kusan dukkanin daraktocin hukumar abun ya shafa kamar yadda wata majiya mai tushe ta shaida mana, lamarin da ya jijjiga mutane da dama da ake ganin Minista mai barin gado ya jijjija hukumar.
Kabiru Yusuf Mohammed, dai yana da kwarewa sosai a bangaren kula da filayen jiragen sama da yayi aiki a fannoni daban na gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.