Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya yaba wa Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal bisa jajircewarsa da ci gaba da bayar da goyon baya ga ayyukan soji a jihar.
A ranar Alhamis ɗin nan ne ministan ya ziyarci gidan gwamnatin Zamfara da hedikwatar rundunar haɗin gwiwa ta ‘Operation Fansar Yamma’ da ke Gusau.
- Xi Jinping Ya Gana Da Shugabannin Masar Da Iran
- TCN Ta Gano Dalilin Katsewar Wutar Lantarki A Arewacin Nijeriya, Ta Fara Gyara
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa ziyarar na da nufin inganta haɗin gwiwa tsakanin jihar da ma’aikatar tsaro.
Sanarwar ta ƙara da cewa, ministan ya tattauna batutuwan da suka shafi ziyarar da gwamna Lawal da gwamna Raɗɗa suka kai Ma’aikatar Tsaro a farkon makon nan.
A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya jaddada aniyar gwamnatinsa na bayar da haɗin kai ga dukkanin hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a Zamfara.
“Ina so in miƙa godiyata ga Ministan Tsaro, wanda ya zo yau domin tattauna batun matsalar tsaro a Zamfara.
“Kwanaki kaɗan da suka gabata ni da gwamnan jihar Katsina muka je ofishin minista a Ma’aikatar Tsaro, inda muka tattauna batutuwa masu muhimmanci.
“Bayan kwana biyu, ministan ya zo wurinmu. Wannan abin a yaba ne na irin ƙwazon da ministan ya nuna.
“Zamfara na fuskantar ƙalubalen tsaro da dama, amma a matsayinmu na gwamnati mai cikakken iko, duk mun tashi tsaye don neman taimako da haɗa kai da hukumomin tsaro. Mun himmatu wajen ba da dukan taimako ga sojoji.
“Za mu kai yaƙi ne ga ‘yan bindigar saboda kare kanmu. Abin da na gani zuwa yanzu ya nuna cewa batun ‘yan bindiga zai zama tarihi in Allah Ya yarda.
“Na yi alƙawari ga ministan. Bugu da ƙari, na saya wa sojoji motocin da harsashi ba ya fasa su guda goma. Haka kuma akwai sauran kayan aikin da za a ba jami’an tsaro domin taimaka musu wajen yaƙar ‘yan bindiga.
“Idan za mu iya magance ƙalubalen ‘yan bindiga a Zamfara, za a magance kashi 90 na matsalar jihar.
“Ina kira ga jami’an tsaro, musamman sojoji, cewa muna buƙatar su. Ina da yaƙinin suna da abin da ake buƙata don kawar da ‘yan ta’adda.
“Na yi alƙawari, kuma ina tare da ku. Ina godiya ga kowa da kowa, musamman Minista da ke ba da lokacin zama tare da mu.”
A farko dai, Ministan Tsaro, Alhaji Badaru Abubakar, ya ce nasarorin da ake samu a yaƙi da ‘yan bindiga na da alaƙa da ci gaba da goyon bayan gwamnatin Gwamna Lawal.
“Mun fara ganin an samu ci gaba, sakamakon goyon bayan Gwamnan Jihar Zamfara.
“Gwamnan ya samar da masauki ga kwamandojin soji, wuraren horo, kyamarori masu sa ido na nesa, motoci, da dai sairan kayan aiki. Har ma ya bai wa sojojin motocin yaƙi. Ranka ya daɗe, mun gode maka sosai.”