• English
  • Business News
Friday, September 12, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ministan Tsaro Ya Yi Gargadin Sake Dawowar Boko Haram Na Barazana Ga Nijeriya

by Yusuf Shuaibu and Sulaiman
3 months ago
in Labarai
0
Ministan Tsaro
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Ministan tsaro, Mohammed Badaru, ya yi gargadin cewa dawowar mayakan Boko Haram a Arewa Maso Gabas, musamman a Jihar Borno, wani babban barazana ce ga zaman lafiyar a yankin Sahel da ya hada da Nijeriya, Jamhuriyar Nijar, Burkina-Faso da Mali.

Badaru ya bayyana gargadin ne a lokacin ziyarar aiki na kwana biyu a sassanin soja na Jihar Kaduna. Ministan ya bayyana haka ne ga ‘yan jarida jim kadan bayan ziyartar sassanin sojojin.

  • Ma’aikatar Harkokin Waje: Kasar Sin Ta Kasance Gwarzuwa Wajen Samar Da Ci Gaba Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba
  • Shugabannin Sin Da Amurka Sun Tattauna Ta Wayar Tarho

“Idan kana bin abin da ke faruwa a Jamhuriyar Nijar, Burkina Faso, da Mali, za ka ga cewa wadannan hare-haren sun karu a ko’ina.

“Akwai alama da ke nuna cewa mayakan sun dawo da karfinsu a yankin Sahel, sannan muna yin duk mai yiwuwa wajen sake tunkarar su,” in ji Badaru.

Ministan ya kara da cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da yaki da wadannan ‘yan ta’adda, yayin da ya nuna kwarin gwiwa cewa za a samu zaman lafiya mai dorewa cikin wannan yanki.

Labarai Masu Nasaba

Hasashen Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Kaduna Ta Ƙaddamar Da Shirin Ko-ta-kwana

Gwamnan Kebbi Ya Dakatar da Kwamishinan Ma’aikatar Lafiya Biyo Bayan Sakaci A Aiki

“Idan za ku yi adalci a gare mu, a cikin makonni biyu da suka gabata, za ku ga cewa sojojin suna samun nasara wajen karya lagon ‘yan ta’adda, inda suka kashe su tare da tarwatsa sassaninsu,” in ji ministan.

A karshen makon da ya gabata, wadanda ake zargi ‘yan ta’adda na Boko Haram sun dasa na’urorin fashewa a Unguwar Guzamala na Jihar Borno, inda suka kashe mutane tara.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Sarki Sanusi II Ya Soke Hawan Sallah, Ya Bayyana Dalili

Next Post

Kar Ki Bari Naman Sallah Ya Kashe Miki Aure Yar’uwa

Related

Hasashen Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Kaduna Ta Ƙaddamar Da Shirin Ko-ta-kwana
Labarai

Hasashen Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Kaduna Ta Ƙaddamar Da Shirin Ko-ta-kwana

2 hours ago
Gwamnan Kebbi Ya Dakatar da Kwamishinan Ma’aikatar Lafiya Biyo Bayan Sakaci A Aiki
Labarai

Gwamnan Kebbi Ya Dakatar da Kwamishinan Ma’aikatar Lafiya Biyo Bayan Sakaci A Aiki

3 hours ago
Shettima
Labarai

Shettima Ya Bada Umarnin Gaggauta Raba Lamunin Naira Biliyan 250 Ga Ƙananan Manoma 

4 hours ago
Rashin Tsaro: Zanga-zanga Ta Ɓarke A Jihar Kogi 
Labarai

Rashin Tsaro: Zanga-zanga Ta Ɓarke A Jihar Kogi 

5 hours ago
Boko Haram Na Yin TikTok, Suna Sarrafa Jirage Marasa Matuƙi Don Sa Ido Kan Sansanonin Soji – Bulama 
Labarai

Ƙwararren Masanin Tsaro, Bulama Ya Ƙaryata Iƙirarin El-Rufai Kan Biyan ’Yan Bindiga Kuɗaɗen Fansa

6 hours ago
Gwamnatin Tarayya Ta Ɓullo Da Kwasakwasai 26 Na Kasuwanci Don Rage Yawan Masu Neman Aikin Gwamnati
Manyan Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Ɓullo Da Kwasakwasai 26 Na Kasuwanci Don Rage Yawan Masu Neman Aikin Gwamnati

7 hours ago
Next Post
aure

Kar Ki Bari Naman Sallah Ya Kashe Miki Aure Yar'uwa

LABARAI MASU NASABA

Hasashen Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Kaduna Ta Ƙaddamar Da Shirin Ko-ta-kwana

Hasashen Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Kaduna Ta Ƙaddamar Da Shirin Ko-ta-kwana

September 11, 2025
Gwamnan Kebbi Ya Dakatar da Kwamishinan Ma’aikatar Lafiya Biyo Bayan Sakaci A Aiki

Gwamnan Kebbi Ya Dakatar da Kwamishinan Ma’aikatar Lafiya Biyo Bayan Sakaci A Aiki

September 11, 2025
Za A Gudanar Taron Tattaunawa Karo Na 12 Na Dandalin Xiangshan A Nan Birnin Beijing

Za A Gudanar Taron Tattaunawa Karo Na 12 Na Dandalin Xiangshan A Nan Birnin Beijing

September 11, 2025
Shettima

Shettima Ya Bada Umarnin Gaggauta Raba Lamunin Naira Biliyan 250 Ga Ƙananan Manoma 

September 11, 2025
An Zabi Wuraren Ban Ruwa Hudu Na Kasar Sin Domin Shigar Da Su Jadawalin Wuraren Ban Ruwa Na Kasa Da Kasa

An Zabi Wuraren Ban Ruwa Hudu Na Kasar Sin Domin Shigar Da Su Jadawalin Wuraren Ban Ruwa Na Kasa Da Kasa

September 11, 2025
Rashin Tsaro: Zanga-zanga Ta Ɓarke A Jihar Kogi 

Rashin Tsaro: Zanga-zanga Ta Ɓarke A Jihar Kogi 

September 11, 2025
Shawarar Jagorantar Harkokin Duniya: Mafitar Sin Ga Kasa Da Kasa

Shawarar Jagorantar Harkokin Duniya: Mafitar Sin Ga Kasa Da Kasa

September 11, 2025
Boko Haram Na Yin TikTok, Suna Sarrafa Jirage Marasa Matuƙi Don Sa Ido Kan Sansanonin Soji – Bulama 

Ƙwararren Masanin Tsaro, Bulama Ya Ƙaryata Iƙirarin El-Rufai Kan Biyan ’Yan Bindiga Kuɗaɗen Fansa

September 11, 2025
Wata Mahanga Ta Daban Na Kallon Ayyukan Ta’addanci

Wata Mahanga Ta Daban Na Kallon Ayyukan Ta’addanci

September 11, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Ɓullo Da Kwasakwasai 26 Na Kasuwanci Don Rage Yawan Masu Neman Aikin Gwamnati

Gwamnatin Tarayya Ta Ɓullo Da Kwasakwasai 26 Na Kasuwanci Don Rage Yawan Masu Neman Aikin Gwamnati

September 11, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.