Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana cewa kasar Sin ta dukufa sosai ga samar da ci gaba ta hanyar babban matakin bude kofa kuma za ta ci gaba da ba da kulawa ga yanayin kasuwanci da ya dace da kasuwa, bisa doka kuma irin wanda zai zama na duk duniya, da karfafa hadin gwiwar “Ziri Daya da Hanya Daya” mai babban inganci tare da aiwatar da shirin Bunkasa Ci Gaba.
Wang ya bayyana haka ne a jiya Laraba, a wani taron tallatawa da ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta karbi bakuncinsa domin gabatar da Tashar Tekun Kasuwanci Maras Shinge ta Hainan ga duniya.
- Amfani Da Salon Diflomasiyyar Kasar Sin Zai Iya Sulhunta ECOWAS Da Kasashen Nijar, Mali Da Burkina Faso Cikin Sauki
- Adadin Zirga Zirga Ta Jiragen Kasa A Sin Ya Haura Biliyan 4 A Watanni 11 Na Farkon Bana
A watan Yunin 2020 ne kasar Sin ta fitar da wani babban tsari da nufin gina daukacin tsibirin Hainan ya zama mai alfanu ga duniya da kuma samar da babbar tashar teku ta kasuwanci maras shinge zuwa tsakiyar karnin da muke ciki.
Wanga ya kara da cewa, Tashar Tekun Kasuwanci Maras Shinge ta Hainan ta zama wani sabon babi na bude kofar kasar Sin, da zama wurin da ya kamata a yi rige-rige wajen cin gajiyar hadin gwiwa da juna, kana da kasancewa sabon ginshikin tafiyar da dunkulewar tattalin arzikin duniya.
Ministan ya ba da tabbacin kasar Sin za ta ci gaba da bin matakin samun bunkasa kofa a bude, mai sabbin kirkire-kirkire, da lafiya ga muhalli, mai hadaka kuma cikin zaman lafiya da lumana. (Abdulrazaq Yahuza Jere)