Ministan harkokin wajen kasar Mali Abdoulaye Diop ya bayyana cewa, kasar Sin tana daukar ‘yancin rayuwa da samun ci gaba a matsayin muhimman hakkokin dan Adama, kana tana bisa tafarkin da ya dace wajen raya hakkin dan-Adam cikin nasara, wannan shi ne abin da kasashen yankin Sahel ya dace su yi koyi da shi.
Diop ya bayyana haka ne a yayin bude taron karawa juna sani game da “yancin rayuwa da ci gaba su ne muhimman abubuwa game da raya hakkin dan-Adam a kasashen yankin Sahel” da aka gudanar a wannan rana. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)