Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi a ranar Juma’ar nan, ya yi kira ga kasashen da ke cikin kungiyar G20 da su yi aiki tare don gina duniya mai adalci da ci gaba na bai-daya.
Wang ya bayyana hakan ne yayin jawabinsa a rana ta biyu na taron ministocin harkokin wajen kasashen G20, a birnin Johannesburg.
Wang ya bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da dukkan bangarori domin aiwatar da manufar taken shugabancin kungiyar na kasar Afirka ta Kudu mai lakabin “Hadin kai, daidaito, da dorewa”, tare da bude wani sabon babi na hadin gwiwar G20, da hada karfi da karfe don gina duniya mai adalci mai kunshe da ci gaba na bai-daya.
Wang ya kara da cewa, Afirka na fuskantar wani sabon zango na farkawa, wanda ya kamata a yayin gudanar da taron na G20 a kara samar da albarkatun raya kasa, da tallafa wa hadin gwiwar ayyukan bunkasa ci gaban kasa da kasa, da hada kai da Afirka a fannonin masana’antu, da kayayyakin more rayuwa, da albarkatu marasa gurbata muhalli, da kuma hanzarta hawa turbar zamanantarwa.
A ranar Juma’a ce Afirka ta Kudu ta kammala taron ministocin harkokin wajen kasashen G20, bayan an tattauna batutuwa da dama da suka shafi duniya.
Taron na farko na ministocin harkokin wajen G20 a karkashin shugabancin Afirka ta Kudu ya kasance mai cike da tarihi, domin shi ne taron ministocin wajen kungiyar na farko a nahiyar Afirka, kamar yadda ministan huldar kasa da kasa da hadin gwiwa na Afirka ta Kudu, Ronald Lamola ya bayyana, yayin da yake yabawa da taron, a wani taron manema labarai bayan kammala taron, inda har ila yau ya kara da cewa, taron “mai matukar fa’ida” ya yi gagarumar tattaunawa a kan dabarun da suka shafi yanayin shiyyoyin duniya da tasirinsu a kan gudanar da ayyukansu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)