Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ƙaddamar da shafin kundin yada labarai da bayar da bayanai na Gwamnatin Nijeriya a matsayin wata babbar hanyar sadarwa ta zamani don samun cikakkun bayanai game da ƙasar.
Idris, wanda ya ƙaddamar da shafin a lokacin da aka fara gabatar da bayanai na Ayyukan Ministoci don bikin cikar gwamnatin Tinubu shekara ɗaya, ya ce gidan yanar wata cibiya ce da aka ware domin mutanen cikin gida da na ƙasashen waje, don samar da sababbi kuma amintattun bayanai kan abubuwa daban-daban na al’amuran ƙasa da suka haɗa da gwamnati, al’ummar Nijeriya, al’adun su da dai sauran su.
- Wata Sabuwa: Wani Alkali Daga Amurka YA Dakatar Da Sake Nada Sarki Sanusi II
- Bukatar Lalubo Hanyoyin Cin Gajiyar Ma’adinai A Nijeriya
Ya ce: “Muna amfani da wannan damar wajen ƙaddamar da shafin kundin labarai na yanar gizo na Yaɗa Labarai na Nijeriya. Tabbas, akwai shi a baya amma ba a kula da shi da kyau ba har Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta sake farfaɗo da wannan sabon shafin.
“Hanya ce ga duk bayanan da kuke buƙatar sani game da wannan gwamnati; game da Nijeriya, mutane, da al’adun mu. Don haka, mu gode wa gwamnatin Nijeriya da ta sake buɗe wannan sabon gidan yanar yaɗa labarai na ƙasa.”
Shafin shi ne kamar haka: www.nigeria.gov.ng.
Tun da fari da yake gabatar da jawabin buɗe taron, ministan ya ce Shugaban Ƙasa ya soma kafa ginshiƙi mai nagarta kuma mai ɗorewa wanda zai inganta rayuwar jama’ar Nijeriya.
Ya ce: “Manyan shirye-shirye irin su Hukumar Bada Lamuni ga Masu Sayayya, Gidauniyar Lamunin Ilimi ta Nijeriya, Shirin Shugaban Ƙasa na Samar da Iskar Gas, Shirin Shugaban Ƙasa na Bada Lamuni na Naira Biliyan
200, ƙoƙarin mu na Aikin Goma da Ba da Tsaro domin Samar da Abinci (wanda ya haɗa da ƙaddamar da Noman Rani, da gagarumin aikin raba takin zamani), Shirin Haɓaka Wuraren Ayyuka na Sabuwar Fata, (RHIDF), Shirin Birane da Gidaje na Sabuwar Fata, ayyukan mu na yin gyara a Fannin Wutar Lantarki, da kuma ɓangaren Tsarin Haraji da Hada-hadar Kuɗi, da tattaunawar da ake yi na za a samar da albashi mafi ƙaranci na ƙasa, – suna daga cikin manyan tsare-tsare da shirye-shirye masu yawa waɗanda kai-tsaye za su shafi rayuwa da hanyoyin samun kuɗin shiga kuma su inganta rayuwa da abincin miliyoyin ‘yan Nijeriya.”