Karamar ministar ma’adanai a gwamnatin Buhari, Gbemi Saraki, ta musanta rade-radin ficewa daga jam’iyyar APC.
Tsohuwar Sanatan ta Kwara, ta ce ikirarin sauya shekar ta zuwa jam’iyyar PDP, labari ne na karya.
- Dalilin Da Ya Sa Kwankwaso Bai Taya Tinubu Murnar Lashe Zabe Ba –NNPP
- ECOWAS Za Ta Karrama Buhari Da Lambar Yabo
Dan uwan Gbemi, Bukola Saraki, wanda tsohon gwamnan Kwara ne kuma shugaban majalisar dattawa, ya koma jam’iyyar PDP watanni kafin zaben 2019.
Wata sanarwa da mai magana da yawun ministar, Moses Bello, ta fitar ta musanta cewa a yanzu tana adawa da dan takarar gwamnan PDP, Shuaibu Yaman.
Saraki ta tunatar da yadda ta yi aiki tukuru domin ganin zababben shugaban kasa Bola Tinubu ya lashe zaben shugaban kasa a jihar.
Ta ce hakan ya faru ne duk da rashin jituwa da ayyukan gwamnatin jihar karkashin jam’iyyar APC dangane da gadon marigayi Olusola Saraki.
“Idan har wani abu, na kara himma wajen tabbatar da nasarar gwamnatin Asiwaju da Shettima mai zuwa a ranar 29 ga Mayu,” in ji ministar.
Bello ta kara da cewa, Gbemi Saraki ta kasance mai wayar da kan jama’a tare da ci gaba da biyayya ga gwamnatin shugaba Buhari da kuma gwamnati mai jiran gado.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp