Hukumar ƙwallon ƙafa ta Morocco (FRMF) ta shigar da takardar ƙorafi a hukumance zuwa hukumar ƙwallon ƙafa ta Afrika (CAF), tana zargin “rashin adalci daga alƙalin wasa” a wasan ƙarshe na gasar cin kofin mata ta Afrika (WAFCON) da aka fafata tsakaninta da Super Falcons ta Nijeriya.
Kamar yadda jaridar Morocco World News ta ruwaito, FRMF ta bayyana cewa alƙaliyar wasan ta fasa bayar da hukuncin bugun daga kai sai mai tsaron gida (penalty) a minti na 82 da wasan ke 2-2, wanda suka ce ya kamata a baiwa tawagar su.
- Sin: Ya Kamata A Warware Sabanin Tattalin Arziki Da Cinikayya Ta Hanyar Tattaunawa
- Matashi Ya Kashe Surukarsa Saboda Shigarta Cikin Sha’anin Aurensu
Bidiyon da aka sake dubawa ya nuna yiwuwar cewa ƴar wasan baya ta Nijeriya, Tosin Demehin, ta taɓa ƙwallo da hannu, amma bayan nazarin na’urar VAR, alƙaliyar ta soke hukuncin farko da ta yanke. Wannan mataki ya fusata ‘yan wasan Morocco da masu horas da su, inda suka ce hakan ya shafi sakamakon wasan da Nijeriya ta samu nasara da ci 3-2.
Kocin Morocco, Jorge Vilda, wanda ya jagoranci ƙasar Spain zuwa nasara a gasar cin kofin duniya ta mata a 2023, ya bayyana cewa: “Ƙaramin kuskure ne ya sa muka rasa wasan.” Duk da cewa bai saba magana kan alƙalanci ba, Vilda ya amince cewa gajiya ta taka rawa a durƙusar da tawagarsa a zagaye na biyu.
A nasa ɓangaren, kocin Nijeriya, Justine Madugu, ya yabawa Morocco bisa ƙoƙarin da suka nuna a rabin lokacin farko, yana mai cewa sauye-sauyen da suka yi a rabin lokaci na biyu ne suka sauya akalar wasan.
A cewarsa: “Canje-canjen sun taka muhimmiyar rawa.” An buga wasan ƙarshe a filin wasa na Rabat Olympic Stadium, inda Morocco ta fara da ci 2-0, amma Nijeriya ta dawo da ƙwallaye daga Esther Okoronkwo, Folashade Ijamilusi, da ƴar canji Jennifer Echegini. Wannan nasara ta baiwa Super Falcons nasarar lashe kofin WAFCON karo na 10 – mafi yawa a tarihin gasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp