Morocco za ta sake kardaar bakuncin kofin Afrika na Mata WAFCON karo na uku a jere a 2026, yayin da aka sanar da wasannin share fagen shiga gasar a ranar Alhamis kuma kasashe 38 ne za su fara fafatawa a gasar, an samu ragin kasashe hudu da za su buga gasar 2024.
Kowacce kasa za ta buga wasa biyu – gida da waje, domin samun 11 da za su hadu da mai masaukin baki su buga gasar Wafcon ta 2026, sannan kasashe shida da ke saman jerin jadawalin Afrika da suka hada da Nijeriya da South Africa da Ghana da Cameroon da kuma Ibory Coast, za su samu tikitin zuwa zagaye na biyu ko da ba su fafata ba.
- Ko Me Ke Kawo Yawan Tashin Gobara A Wannan Lokaci Na Hunturu?
- Kudirin Dokar Haramta Amfani Da Kudaden Waje Ya Tsallake Karatu Na Farko A Majalisa
Za a yi wasan zagaye na farko ne a watan Fabirairun 2025, sannan a yi na biyu a watan Oktoban shekarar mai zuwa sai dai har yanzu dai hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF ba ta sanar da ranar da za a fara gasar ba.
Botswana da Dr Congo da suka je matakin karshe na 2024 bai zama dole su halarci gasar ta 2026, saboda koma bayan da suka fuskanta kuma za su kara da juna a wasan farko sannan wanda ya yi nasara zai fuskanci gwarzuwar gasar Afrika ta Kudu.
Gasar Wafcon ta 2024 da za a yi a Mkoocco aka jinkirta za a gudanar da ita ne daga ranar 5 ga watan Yuli zuwa 26 na shekara mai kamawa, saboda matsar da ita baya da aka yi saboda gasar Olympics ta 2024 da aka yi a birnin Paris.
Jadawalin wasannin shiga gasar Afrika ta mata ta 2026
Wasannin zagayen farko
Angola da Zimbabwe sai Malawi da Congo-Brazzadaille. Botswana da DR Congo Tanzania da Ekuatkoial Guinea- Uganda da Ethiopia – Eswatini da Namibia Burundi da Burkina Faso – Djibouti da Togo – South Sudan da Algeria – Rwanda da Egypt Kenya da Tunisia Niger da Gambia Benin da Sierra Leone – Guinea da Cape – DAerde Gabon da Mali – Chad da Senegal.
Za a yi wasannin gida da wajen ne daga ranar 17 ga watan Fabirairun 2025 zuwa 26
Wasannin zagaye na biyu
Angola ko Zimbabwe da Malawi ko Congo-Brazzadaille, Botswana ko DR Congo da South Africa – Tanzania ko Ekuatkoial Guinea da Uganda ko Ethiopia – Eswatini ko Namibia da Zambia- Burundi ko Burkina Faso da Djibouti ko Togo South Sudan ko Algeria da Cameroon Rwanda ko Egypt da Ghana- Kenya ko Tunisia da Nijar ko Gambia – Benin ko Sierra Leone da Nijeriya – Guinea ko Cape Barde da Gabon ko Mali
Chad ko Senegal da Ibory Coast.
Za a yi wasannin gida da wajen ne daga ranar 20 ga watan Oktoba 2025 zuwa 28