Majalisar Dinkin Duniya ta ce a karon farko cikin watanni hudu wani ayarin motocin agaji ya shiga kasar Sudan daga kasar Chadi domin kai kayan abinci da ake bukata ga mutanen da ke fuskantar barazanar yunwa a yankin Darfur.
Sama da manyan motoci 12 ne suka tsallaka kan iyaka a Adré mako guda bayan da gwamnatin sojan ta amince ta ba da agaji.
Sojojin sun rufe iyakokin ne a wani yunkurin da suka ce na dakatar da kai wa dakarun RSF makamai.
Sama da mutum miliyan goma ne suka rasa matsugunansu tun bayan fara yaki a watan Afrilun bara.
Fiye da kuma mutum miliyan 25 kwatankwacin rabin al’ummar Sudan kenan na fuskantar matsananciyar yunwa.
Kasashen duniya na ci gaba da kokri domin ganin bangarorin biyu sun gana tare da amincewa da tsagaita bude wuta