Connect with us

RAHOTANNI

Mu Hada Kai Don Ba Mu Da Kasar Da Ta Fi Nijeriya – Sarkin Fulanin Ijobo

Published

on

Sarkin Fulanin yankin Ijobo da ke Legas, Alhaji Sali Sa’adu ya bayyana cewa ba su da wata kasa a duk duniyar nan da za su yi tinkaho da ita kamar Nijeriya.

Yana wannan jawabi ne a fadarsa da ke rukunin gidajen Jakande da ke Legas. Alhaji sali sa’adun ya yi adu’ar fatan alkhairi da kuma wannan cuta ta Korona Allah ya kawo saukinta a Nijeriya da duniya baki daya.

Sarkin fulanin kuma galadiman ijobo Legas ya roki “Yan Nijeriya su hada kai da taimaka wa juna, “kuma mu bawa shugabanni shawara ta gaskiya domin ci gaban wannan kasa tamu Nijeriya,” in ji shi.

Galadiman na Ijobo ya kuma roki ‘yan arewa maza da mata a duk inda suke su rika hada kai da karin zumunci a tsakaninsu da kuma sauran abokan zamansu na jihohin yamma domin taimaka wa bunkasa ci gaban Nijeriya.

Ya kuma mika godiya ga abokanan aikinsa irin su Sarkin Hausawan Ijobo Alhaji Muhammadu Ibrahim da mataimakin sarkin hausawan ijobo Abdulhamidu Ibrahim Giddare da ‘yan majalissarsu baki daya, saboda kokarin da suke na ganin an zauna lafiya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: