Bayan da kasar Amurka ta dakatar da bayar da tallafi ga kasashen Afirka, akwai mutanen da suka yi fushi, da wasu da suka fara daukar matakai, amma ba wanda ya yi rokon afuwa.
A kwanakin nan, kasar Amurka ta sanar da kawo karshen kaso 83% na ayyukan da ake tafiyar da su karkashin tsarin hukumar USAID, lamarin da ya haifar da tsaiko ga yarjeniyoyin hadin gwiwa 5200. Dangane da matakai masu alaka da batun, dan jarida a fannin kimiyya da fasaha Abdullahi Tsanni, ya rubuta a cikin wata mukalar da aka wallafa cikin mujallar Science da cewa, “Daukacin kasashen nahiyar Afirka sun yi fushi matuka”, saboda “an soke kudin tallafawa aikin hana yaduwar cututtuka, da yawansa ya kai biliyoyin daloli, da dakatar da gwaje-gwajen fasahohin jinya ba zato ba tsammani, lamarin da ya sanya mutane fiye da dubu dari 1 fuskantar yiwuwar rasa rayuka.”
- Gwamna Buni Ya Naɗa Matasa 200 A Matsayin Hadimansa
- Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutum 6 A Nasarawa
Sai dai bayan nuna takaici, ‘yan Afirka ba su daga tutar amana ko rokon afuwa ba. Maimakon haka, sun fara bincike a kai. Misali, Salim Karim, shugaban cibiyar nazarin cutar kanjamau ta kasar Afirka ta Kudu, ya ce janyewar tallafin Amurka wani gargadi ne ga kasashen Afirka, wanda ya nuna cewa “Kar a dogara da tallafin da sauran kasashen suke bayarwa wajen biyan bukatar kai, dole ne a yi kokarin dogaro da kai.”
A sa’i daya kuma, gwamnatocin kasashen Afirka sun fara daukar matakai. Inda a Najeriya, majalisar dattawa ta zartas da ware karin dalar Amurka miliyan dari 2 don tallafi a bangaren aikin jinya. Kana a kasashen Botswana, da Kamaru, da Kenya, hukumomi masu kula da aikin jinya sun yi alkawarin samar da kudin da ake bukata wajen kula da masu kamuwa da cutar kanjamau, yayin da gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ta yi niyyar samar da kaso 83% na kudin da ake bukata a wannan bangare. Ko da yake akwai wuyar cike dukkan gibin da ke akwai ta fuskar kudin tafiyar da aikin jinya, amma dukkan kasashen Afirka sun nuna niyyar dogaro da kai. Hakan ya dace da maganar da shahararriyar masaniyar ilimin hana yaduwar cututtuka ta kasar Zimbabwe, Francisca Mutapi ta fada, wato “Kasashen yamma ba za su samar da dabarar daidaita matsalar aikin jinya a Afirka daga tushenta ba.”
Ma iya cewa karfin zuciya da kasashen Afirka suka nuna a wannan karo ya burge ni sosai, sai dai bai ba ni mamaki ba. Saboda na dade ina ganin alamar “farkar nahiyar Afirka”, da yadda kasashen Afirka suke daukar matakai bisa muradun kansu. Misali, bayan barkewar yaki tsakanin Ukraine da Rasha, kasashen Afirka sun ki daukar wani bangare tsakaninsu, ko da yake suna fuskantar matsin lamba daga kasashen yamma. Kana a fannin tattalin arziki, kasashen Afirka na kokarin gina wani babban yankin ciniki mai ‘yanci da ya shafi daukacin nahiyar Afirka. Yayin da a fannin tsaro, sun sa sojojin Faransa, da na Amurka janye jiki daga kasashen dake yammacin Afirka daya bayan daya.
Hakika yadda kasar Amurka ta dakatar da tallafi a wannan karo ya nuna ra’ayin shugaba Donald Trump dangane da kasashen Afirka. Wanda za a iya fahimta bisa ganin yadda ya bayyana kasar Lesotho a matsayin “kasar da ba a san ta ba”, wacce ba ta cancanci tallafin da ake ba ta ba, a kwanakin baya, yayin da yake magana da ‘yan majalisun kasar Amurka. Sai dai shugaban bai san sauye-sauyen da kasashen Afirka suka samu ba, wadanda tun tuni suka daina dogaro da kasashen yammacin duniya.
A daura da haka, ana iya ganin fahimtar matsayin kasashen Afirka mai dacewa, a cikin maganar da ministan wajen kasar Sin Wang Yi ya fada a kwanan baya, yayin da yake amsa tambayar da wakiliyar kafar yada labaru ta Najeriya NAN ta gabatar masa. Inda ya bayyana nahiyar Afrika a matsayin wuri mai muhimmanci a karni na 21, wanda samun kwanciyar hankali da ci gaban tattalin arzikinsa ya shafi makomar bai daya ta daukacin dan Adam. Sa’an nan, bayan da ya yi bayani kan kokarin da kasar Sin ta yi wajen haifar da takamaiman ci gaba a kasashen Afirka, jami’in na Sin ya ce, “Nahiyar Afirka na cikin wani sabon mataki na farkawa. Kamata ya yi a mara musu baya, don su iya dogaro da kai wajen tafiya a kan sabuwar turbarsu ta raya kasa.” (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp