A yau Lahadi, aka gudanar da taron fitar da sakamakon nazarin ayyukan kimiyya na yanki mai tsaunuka na Qinghai-Xizang karo na biyu a jihar Xizang mai cin gashin kanta.
Masana daga cibiyar nazarin yanki mai tsaunuka na Qinghai-Xizang na cibiyar nazarin ayyukan kimiyya ta kasar Sin da cibiyar nazarin ayyukan kimiyya na yanayin sama ta Sin da jami’ar Peking da jami’ar Lanzhou da sauransu, sun hadu a birnin Lhasa, fadar mulkin jihar Xizang, don gabatar da babban sakamakon da aka samu kan manyan ayyuka 10 a cikin nazarin ayyukan kimiyya na wannan karo, a shekaru 7 da suka gabata.
- NDLEA Ta Cafke Wani Ɗan Kasuwa Ya Haɗiye Hodar Iblis Ƙulli 88 A Abuja
- Ba Mu Da Masaniya Kan Kwangilar Samar Da Magunguna – Gwamnatin Kano
Nazarin ayyukan kimiyyan ya nuna cewa, a cikin shekaru 15 da suka gabata, muhallin halittu na yanki mai tsaunuka na Qinghai-Xizang yana samun kyautatuwa, daga ciki, fadin ciyayi da dazuzuka masu kyau sun karu da kashi 6 cikin dari da kuma kashi 12 cikin dari, karfin kiyaye tushen ruwa da kiyaye kasa da kuma yaki da iska da kwararowar hamada sun karu da kashi 1 cikin dari da kashi 2 cikin dari da kuma kashi 70 cikin dari, kana karfin ba da kariya ga muhallin halittu ya ci gaba da kyautatuwa a kai a kai.
Bisa sakamakon, a cikin shekaru 7 da suka gabata, masu nazarin ayyukan kimiyya sun tarar da sabbin nau’o’in halittu fiye da 3000, kuma sun sake tarar da wasu nau’o’in halittu da aka yi tsammanin dukkansu sun riga sun mutu ko ba a taba ganinsu ba cikin lokaci mai tsawo.
Ban da hakan, sakamakon nazarin ya bayyana cewa, watakila yau shekaru dubu 190 da suka gabata, mutane sun fara zauna a yanki mai tsaunuka na Qinghai-Xizang. (Safiyah Ma)