• English
  • Business News
Saturday, June 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Muhammad Bashir Ya Zama Sakataren Yaɗa Labaran Ƙungiyar Tsofaffin Ɗaliban AKCILS

by Naziru Adam Ibrahim
6 months ago
in Labarai
0
Muhammad Bashir Ya Zama Sakataren Yaɗa Labaran Ƙungiyar Tsofaffin Ɗaliban AKCILS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Ɗaliban Legal ta ƙasa (AKCILS), ta gudanar da zaɓen sababbin shugabanninta na ƙasa, inda Shugaban Sashen yanar gizo na Jaridar LEADERSHIP Hausa, Muhammad Bashir Aminu, ya yi nasarar samun muƙamin sakataren yaɗa labaran ƙungiyar.

Muhammad Bashir Aminu, ya samu ƙuri’u 61 inda ya yi nasarar doke abokan takararsa da suka hada da Rakiya Lawan me ƙuri’u 53, da Munir Ibrahim Bala, wanda ya samu ƙuri’u 50.

  • Ba Laifi Ba Ne Seyi Tinubu Ya Nemi Takarar Gwamnan Jihar Legas –  Ƙungiyar Matasa
  • Abin Da Ya Sa Na Sa Dokar Ta-ɓaci A Sashen Ilimin Jihar Zamfara – Gwamna Dauda Lawal

Tuni aka rantsar da sabbin shugabannin ƙungiyar na AKCILS, bayan kammala zaɓen da sanar da waɗanda suka yi nasara wanda ya gudana a ranar Laraba 25 ga watan Disamba 2024.

Muhammad Bashir Aminu, gogaggen ɗan jarida ne da ke da ƙwarewar aiki na fiye da shekaru 10, a manyan wurare daban-daban da suka haɗa da gidan talabijin na ƙasa (NTA) da ke birnin tarayya Abuja, da Rukunonin Kamfanin Jaridun Media Trust, masu buga jaridar Daily Trust da Aminiya da Trust TV da kuma Trust Radio.

Ya kuma zama shugaba mai kula da sashen yaɗa labarai na yanar gizo a ɓangaren hausa na rukunonin kamfanin LEADERSHIP, mai shalkwata a birnin tarayya Abuja, da ke buga jaridar LEADERSHIP ta turanci da Hausa, kuma ya mallaki kamfaninsa na kwantaragin aikin jarida da yaɗa labarai mai suna “Al-ihsan Integrated Services”, inda ya ke da ƙyakkyawar alaƙa da manyan gidajen jaridu na ciki da wajen Nijeriya.

Labarai Masu Nasaba

Za A Ci Gaba Da Tunawa Da Aminu Ɗantata A Ɓangaren Taimakon Jama’a — Buhari

Har Yanzu Ba Mu San Inda Za A Binne Dantata Ba — Sakatarensa

A fannin karatu kuwa bayan diplomar da ya yi a Kwalejin Legal, yana da babbar diploma kan dabarun koyarwa (PDE), kuma ya yi digirinsa na farko a Hausa da babbar diflomar gaba da digiri wanda a yanzu yana kan digirinsa na biyu duk a sashen koyar da harsunan Nijeriya na Jami’ar Bayero, da ke Kano.

kasancewarsa tsohon ɗalibin makarantar mai ƙwazo da ƙwarewar aiki a fanninsa na ilimin fassara da editanci a aikin jarida da sha’anin mulki da riƙe muƙamin Shugaban Ƙungiyar Tsofaffin Ɗaliban Kwalejin, da Jami’ar Bayero ta Kano, ana kyautata zaton zaɓarsa a wannan kujerar zai taimakawa Ƙungiya AKCILS, wajen ciyar da ita gaba ta fuskoki da dama

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: LEADERSHIP
ShareTweetSendShare
Previous Post

Sin Ta Bayyana Sakamakon Kidayar Harkokin Tattalin Arziki Karo Na 5

Next Post

Yadda Turmutsutsin Rabon Kayan Abinci Ya Dagula Karsashin Kirsimeti

Related

Bashin Da Ake Bin Nijeriya Ya Kai Tiriliyan 46.25
Labarai

Za A Ci Gaba Da Tunawa Da Aminu Ɗantata A Ɓangaren Taimakon Jama’a — Buhari

1 hour ago
Har Yanzu Ba Mu San Inda Za A Binne Dantata Ba — Sakatarensa
Manyan Labarai

Har Yanzu Ba Mu San Inda Za A Binne Dantata Ba — Sakatarensa

1 hour ago
Tarihin Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (3)
Labarai

Tarihin Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (3)

3 hours ago
An Kai Wa Magoya Bayan Atiku Hari A Gombe
Manyan Labarai

Rasuwar Dantata Babban Rashi Ne Ga Afirka – Atiku

3 hours ago
Rasuwar Ɗantata Babban Rashi Ne Ga Nijeriya –  Shugaban ƘasaTinubu
Manyan Labarai

Rasuwar Ɗantata Babban Rashi Ne Ga Nijeriya –  Shugaban ƘasaTinubu

5 hours ago
Bam Ya Kashe Mutane 4, Ya Jikkata 21 A Yobe
Manyan Labarai

Bam Ya Kashe Mutane 4, Ya Jikkata 21 A Yobe

6 hours ago
Next Post
Yadda Turmutsutsin Rabon Kayan Abinci Ya Dagula Karsashin Kirsimeti

Yadda Turmutsutsin Rabon Kayan Abinci Ya Dagula Karsashin Kirsimeti

LABARAI MASU NASABA

Kokarin Zamanantar Da Sin Da Afrika Na Kara Karfafa

Kokarin Zamanantar Da Sin Da Afrika Na Kara Karfafa

June 28, 2025
Bashin Da Ake Bin Nijeriya Ya Kai Tiriliyan 46.25

Za A Ci Gaba Da Tunawa Da Aminu Ɗantata A Ɓangaren Taimakon Jama’a — Buhari

June 28, 2025
Har Yanzu Ba Mu San Inda Za A Binne Dantata Ba — Sakatarensa

Har Yanzu Ba Mu San Inda Za A Binne Dantata Ba — Sakatarensa

June 28, 2025
Hukumar NPA Na Son Tara Kuɗaɗen Shiga Naira Tiriliyan 1.2 A 2025

Hukumar NPA Na Son Tara Kuɗaɗen Shiga Naira Tiriliyan 1.2 A 2025

June 28, 2025
An Horas Da Kwararrun Ma’aikata Sama Da Dubu 500 Karkashin Hadin Gwiwar Sin Da Sassan Kasa Da Kasa A Fannin Inganta Kwarewar Ma’aikata

An Horas Da Kwararrun Ma’aikata Sama Da Dubu 500 Karkashin Hadin Gwiwar Sin Da Sassan Kasa Da Kasa A Fannin Inganta Kwarewar Ma’aikata

June 28, 2025
Tarihin Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (3)

Tarihin Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (3)

June 28, 2025
An Kai Wa Magoya Bayan Atiku Hari A Gombe

Rasuwar Dantata Babban Rashi Ne Ga Afirka – Atiku

June 28, 2025
Sin Ta Samu Nasarorin A Zo A Gani Wajen Yaki Da Miyagun Kwayoyi

Sin Ta Samu Nasarorin A Zo A Gani Wajen Yaki Da Miyagun Kwayoyi

June 28, 2025
Kula Da  Kanki Bayan Haihuwa Abu Ne Muhimmi 4

Kula Da  Kanki Bayan Haihuwa Abu Ne Muhimmi 4

June 28, 2025
Mata Ku Kula Da Masu Tallan Maganin Hana Kishiya

Mata Ku Kula Da Masu Tallan Maganin Hana Kishiya

June 28, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.