Kwamishinan ma’aikatar aikin gona na Jihar Kebbi, Barista Attahiru Maccido ya ce, kashi 80 cikin 100 na manoman jihar kananan manoma ne da ke bukatar ilimin zamani domin inganta harkarsu ta noma.
Maccido ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da a ofishinsa a Birnin Kebbi, inda ya shawarci manoman jihar su tashi tsaye wajen yin amfani da kayayyakin zamani domin inganta harkarsu ta noma.
- 2023: Atiku Ya Sha Alwashin Ƙara Wa Jihohi Da Ƙananan Hukumomi Ƙarfin Iko
- ’Yar Kasuwa Elizabeth Homes: Labarin Tashe Da Rushewarta (I)
Maccido n ya ce noma hanya ce ta yin arziki inda wadansu jama’a suka dauke shi sana’ar wahala, inda ya ce, yanzu kasashen waje sun yi nisa wajen inganta sana’ar noma daga yadda ake yin sa a shekarun baya zuwa na zamani.
A cewarsa, ya zama wajibi manoma su tashi tsaye wajen inganta wannan sana’a tasu, da kuma su daukart fannin a matsayin sana’a domin ta haka ne za su rika bin duk hanyoyin da suka dace wajen inganta noman.
Kwamishina ya kara da cewa, Thailand ce da ta shahara wajen noman shinkafa da samar da abinci a duniya amma kuma abin mamaki, kasar ba ta da rabin kasar noma irin wadda Allah ya ba Nijeriya.
Ya sanar da cewa, saboda yin amfani da bincike da kimiyya yanzu Thailand tana kan gaba wajen samar da abinci ga kasashen duniya mu ma Jihar Kebbi haka muke son mu zama a kan gaba a cikin kasashen duniya masu alfahari da aikin noma.
Ya ce, tun ranar da Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin noma a jihar Kebbi aikin noma ya farfado saboda ko an mika ragamar aikin noma ga mai kishin kasa da son jama’a su zama masu dogaro da kansu domin samun karin arziki.
Kwamishinan ya ce, gwamnatin jihar Kebbi tana kokari wajen taimaka wa manoman jihar da dabarun zamani da za su taimaka musu domin inganta noma a fadin jihar.
Ya ce, ko a kwanakin baya gwamnatin jihar ta raba wa manoma kudin tallafin yin noman rani.
Kwamishinan ya ci gaba da cewa, manoma 8,600 suka samu bashin Naira dubu 150 kowanensu, inda ya kara da cewa, a shekara uku da suka wuce, manoman shinkafa dubu 120 suka amfana da tallafin yin noma, sai manoman waken suya dubu biyar da suka amfana da shirin ba da tallafin noma, manoma alkama manoma dubu 1600 gwamnatin jihar ta ba rancen noman alkama.
Ya ce, gwamnatin jihar ta raba wa manoma jihar fiye da Naira biliyan 15, inda ya ce, yanzu haka ta sayo taraktocin noma 100 da kananan taraktoci da ake kira Power Tiller guda 80.
Ya ce, a yanzu suna da taki fiye da tan 100 na taki NPK sai tan 100 na Yuriya domin raba wa manoman rani, an kuma ware naira miliyan 300 domin raba wa masunta a jihar, inda ya sanar da cewa, gwamnatin jihar ta sayo injinan casar shinkafa guda 150 domin raba wa mata.