Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da jawabi ga al’umman kasa cikin bukukuwan ranar samun ‘yancin kai karo na 64, inda ya ce, sabbin manufofi da tsare-tsarensa sun fara ba da sakamakon da ake nema.
Ya kuma sanar da aniyar gwamnatinsa na shigo da matasa a dama da su a cikin gwamnatinsa da ba su damarmaki ta hanyar gudanar da babban taron matasa na kasa na kwanaki 30.
Ga muhimman abubuwa 10 da jawabin Tinubu ya kunsa kamar haka:
Amincewa Da Matsalolin Da Suke Jibge: Tinubu ya ce, yana sane da irin yadda ‘yan Nijeriya da dama ke shan wahalar tsadar rayuwa, tsadar kayan abinci da matsalar rashin ayyukan yi. Ya ba da tabbacin shawo kansu.
Jajircewa: Tinubu ya yi tsokaci kan ci gaban da Nijeriya ta samu tun bayan samun ‘yancin kai, ya lura kan cewa kasar ta samu tsayuwa da kanta duk da rikice-rikice irinsu yakin basasa, da dai sauransu.
Yunkurin Samar Da Tsaro: Ya bayyana muhimman nasarorin da ake samu wajen yaki da ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane, da sauran nau’ikan ayyukan ta’addanci. Ya samar da kashe sama da kwamandoji 30 na Boko Haram da sauran kungiyoyin masu dauke da bindigogi.
Farfado Da Tattalin Arziki: Tinubu ya jaddada wajibcin yin garambawul ga tsare-tsaren tattalin arzikin domin shawo kan matsalolin da suke jibge a sha’anin kudi. Ya ce wannan yunkurin ya kai ga janyo dala biliyan 30 na zuba hannun jarin kasashen waje da kuma inganta hada-hadar kudade.
Yunkurin Rage Matsin Rayuwa: Tinubu ya amince da irin wahalar da jama’a ke sha da matsin rayuwa, musamman kan tsadar farashin kayayyakin abinci, har ma ya ce, “Babban abun da ya fi damun mutanenmu a yau shi ne tsadar rayuwa, musamman kan kayayyakin abinci. Wannan lamarin ya shafi mutane da dama a fadin duniya, inda farashin da tsadar rayuwa ke ci gaba da faruwa a fadin duniya. “Muna sa ran ganin an samu karin amfanin da ake fitarwa da kuma raguwar tsadar kayan abinci.
Samar Da Ayyuka Ga Matasa: Shugaban ya sanar da shirin gudanar da babban taron matasa na kasa da kuma wasu shirye-shiryen da aka ware su kai tsaye ga matasa ciki kuwa har da shirin 3MTT na baje fasaha da kuma asusun rancen ilimi na Nijeriya. “Wannan babban taron zai taimaki matasanmu su samu shiga a dama da su a cikin gudanar da mulki.”
‘Yancin Cin Kashin Kan Kananan Hukumomi A Bangaren Kudade: Tinubu ya jaddada aniyarsa na aiwatar da hukuncin umarnin kotun koli na bai wa kananan hukumomi kason kudadensu kai tsaye.
Shirye-shirye Kan Makamashi Da Sufuri: Ya sanar da shirinsa na fadada rungumar motocin da ke amfani da iskar gas. Ya ce, “Yunkurinmu na kyautata makamashi na tafi kan turba. Muna fadada shirinmu na amfani da motoci masu amfani da iskar gas a bangaren sufuri. Gwamnatin tarayya a shirye take ta mara wa jihohi 36 ciki har da Babban Birnin Tarayya baya da su mallaki motocin domin saukaka wa jama’a sufuri.”
Rage Radadin Annoba Da Matakan Kariya: Shugaban kasa ya kuma yi magana kan yunkurin gwamanti na tunkarar ibtila. Ya ce, “Gwamnatinmu na tunkarar ibtila da aka samu baya-bayan nan, musamman ma na ambaliyar ruwa a wasu sassan kasa. Bayan ziyarar da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya kai Maiduguri, Ni ma da kaina na je na ziyarci garin domin tabbatar wa jama’anmu cewa wannan gwamnatin tarayyar a kowani lokaci tana tare da mutanenta a kowani lokaci. A taron karshe na majalisar koli ta kasa, mun amince da samar da asusun kula da ibtila’i da samar da yanayin da masu kamfanoni da daidaiku za su taimaka mana wajen tunkarar matsaloli cikin gaggawa.
Kyakkyawar Fata Ga Ci Gaba: Ya karkare jawabinsa da karfafan ‘yan Nijeriya da cewa, ka da su yanke kauna, su ci gaba da jajircewa da yin aikin hadin gwiwa domin ci gaba da kuma rayuwar gobe. Ya kuma nanata aniyar gwamnatinsa na kara shigo da kowani bangare da samar da ci gaba mai dorewa da kuma hadin kai.