Alhamdu lillahi. Masu karatu assalamu alaikum wa rahmatullahi ta’ala wa barkatuh. Yau fasalin namu zai yi magana ne kan Fasaha da Balagar harshensa Annabi Muhammadu (SAW).
Dangane da fasahar harshensa da balagar zancensa mai tsira da Amincin Allah, hakika ya kasance cewa kowa ya amince Annabi shi ne gaba, ya fi kowa fasaha da balagar zance domin yana ajiye komai a muhallinsa.
- Sin Ta Bukaci Kwamitin Sulhun MDD Da Ya Ingiza Sassauta Rikicin Lebanon Da Isra’ila
- Ambaliya: Jamus Ta Bai Wa Nijeriya Da Wasu Tallafin Yuro Miliyan 24
Ya fi kowa bayyana lafazi, ya fi kowa ingancin zance, an ba shi kalmomi manya wadanda suka tattare ma’anonin kalmomi da yawa, an kebance shi da hikimomi masu burgewa, an sanar da shi harshen Larabawa duka, yana fahimtar larabcin Yamen, Iraki, Sira, Sham da duk Jaziratul Arab, kuma ya kasance yana magana da duk al’ummar Larabawa, yana mayar mata magana da irin yaren da take magana da shi, kai har yakan yi tserereniya a cikin yaren, har yakan yi karin magana, sau da yawa in ya yi magana sahabbansa ke tambayar shi ma’anar abin da ya fada. Duk wanda ke bibiyar maganganun Annabi (SAW) zai san wannan.
Yana daga cikin fasahar harshen Annabi (SAW), in ka duba maganarsa yayin da wasu Larabawa daga bangare daban-daban kamar yadda ya yi magana da Zim Sha’aril Hamdani, dan kasar Yamen, kabilar Hamdani. Wata rana ya zo wajen Annabi (SAW) bayan ya dawo daga yakin Tabuka da rundunarsa mai yawa, Annabi (SAW) ya yi musu kirari ya ce wadannan su ne Hamdanu masu gaggawar taimako da hakuri wajen yaki, marasa guduwa, ya yi Hijra zuwa Sham a zamanin Sayyidina Umar da mutum 4,000 kuma duk bayinsa ne, bayan ya isa Sham sai ya ‘yanta su bakidaya.
Sai maganar da Annabi ya yi da Ihfatan Nahdi, dan kabilar Nadu, shi ne mafi fasahar mutan Yamen a zamaninsa, shi ne mai magana da yawun kabilarsa da ya samu Annabi suka zanta sai da ya ce ai lalle yau mun hadu da Annabi.
Sai maganar Annadi da Kadani bin Harisatal Ulaimi, shi ne Sahabin da ya nemi Annabi ya yi musu addu’a cewa kasarsu ba su da ruwan sama, a cikin addu’ar akwai fasahohi da balaga mai yawa saboda kasar Balaga za a aika addu’ar.
Sai magana da Annabi 0ya yi da Al’ash’af bin Kaisin Kindi, ya Musulunta a wajen Annabi, bayan rasuwar Annabi (SAW) sai ya yi Ridda, wata rana sai aka kamo shi aka dawo da shi wajen Sayyidina Abubakar. Mutum ne sadauki kuma babba a cikin kabilarshi, Sayyidina Abubakar ya nemi ya kashe shi sai ya ce “Ya Ababakrin bar ni, sabida makiyanka kuma ka aura mun ‘yar uwarka to zan zauna a cikin Musulunci”, Sayyidina Abubakar ya amince da haka, sanadiyyar haka yana daga cikin wadanda suka yada musulunci a Iraki, ya halarci yakukuwan da aka yi a Iraki, ya zauna a Kufa.
Sai maganar da Annabi (SAW) ya yi da Wa’il bin Hijril Kindi, shi ne wanda kafin ya zo Annabi (SAW) ya dinga bushara da zuwansa, sannan ya zo ya musulunta, Annabi ya yi murna da musuluntarsa, saboda Basarake ne na kasar Yamen, Manzon Allah (SAW) ya shimfida masa mayafinsa, ya yi masa addu’ar albarka sannan ya tabbatar da shi akan sarautar Hadramautu.
Manzon Allah (SAW) ya yi magana da mutane da yawa na kabilun Larabawa daga Bangare daban-daban, an kuma ji fasahar da take cikin tattaunawar, kai ka ce Annabi dan kabilar wadanda yake zantawa da su ne.
Duba wasikar Annabi Muhammad (SAW) da ya tura zuwa Kabilar Hamdana “Bayan hamdala da gaisuwa, Duwatsun kasashenku naku ne, ku yi kiwo a cikin kasarku da kwaruruwanta da fakonta wacce za ku ciyar da dabbobinku daga gare ta, idan lokacin Zakka ya zo, abin da za a ba mu na Zakka shi ne Rakuma da Tumaki da abubuwan da ake samu a jikin dabbobin da duk abin da kuka dauka na Amana. Yana daga cikin wajibi a gare ku na daga Zakka kuma abin da ba za mu karba ba: Tsohon Rakumin da hakoransa sun kararraye saboda tsufa da saniyar da ta ragwarbabe saboda tsufa da haihuwa da yayayyen dabba da ragon da ake alfahari da shi. Wacce ake so ku ba da shine dabba cikakkiya ba tsohuwa ba kuma ba yarinya ba.
Sannan kuma ku duba fadarsa ga kabilar Nahdu “Allah ka yi albarka ga Nahdu cikin Madararta, kindirmonta da farau-faranta da take yanzun, Allah ka tura makiwatonta inda akwai kaka – lambu inda ruwa ke kwarara, Allah ka yi albarka cikin dukiyarsu da ‘ya’yansu, duk wanda ya tsaida Sallah a cikinku ya zama Musulumi, duk wanda ya ba da Zakka wannan mai alheri ne, duk wanda ya shaida babu wani sarki sai Allah wannan ya tsarkake, yana gare ku ba ni Nahdi, cika alkawarorin da kuka dauka da mutane lokacin shirka, kar ku yi jayayya wurin ba da Zakka, kar ku yi barna a cikin rayuwa, kar ku dinga yin kasala wajen ba da Sallah” sannan ya rubuta musu a cikin Nisabin Zakka cewa in kun ba mu tsohon dabba ba za mu amsa ba, naku ne wannan, in kun ba mu dan yaye da wacce take kwance Misali wacce ta haihu yanzun ba ta iya tafiya da dabbar da an hore ta mai ita yake hawa – Kamar Doki, ko Rakumi, duk wadannan ba zamu amsa ba naku ne.
Kuma ba za a hana garkenku yin kiwo ba, ba za a yanke manya-manyan bishiyoyinku ba wacce kuke ciyar da dabbobinku, ba za a tsare tumakinku masu Nono ba a ce za a kirga cikin na Zakka, wannan shine alkawarin da yake tsakaninmu da ku muddin ba ku boye munafunci ba kuma ba ku warware alkawari ba, duk wanda ya tabbatar da wannan abu to mu ma za mu cika masa alkawarinsa, wanda yaki to dadi (kari) yana a kansa – za mu kara amsar wani abu bayan mun amsa Zakka (Haraji).
Yana daga cikin hikimomin Annabi (SAW) wasikar da ya tura wa Wa’il bin Hajrin, bayan ya rubuta daga Annabi zuwa Makwayai (Hakimai ko Dagatai) masu girma, masu hasken fuska kuma shuwagabanni. Yana daga cikin abin da ya rubuta a cikin wasikar cewa Zakkar akuyoyi, duk 40 za a ba da akuya ba tsohuwa ko yarinya ba, ba ramammiya ko mai jiki ba, ku bayar da matsakaiciya, a cikin dukiyar da kuka tsinta wacce aka bizne a kasa, daya cikin biyar, wanda ya yi zina na daga saurayi ku yi masa bulala 100, wanda ya yi zina na daga bazawari, ku jefe shi da duwarwatsu, babu sakaci a cikin Addini kuma babu boyewa a cikin Zakkah, duk abin da ke sa maye haramun ne, Wa’il bin Hajrin ya zama shugaban duk Dagatai na Sham.
Wannan maganganu da muke kawo su da yaren Hausa, in an juya su a irin yarensu na Sham ba irin na Kuraishawa ba ko na Mutan Madina, za ka samu lallai Hikima ta cika.
Yayin da maganar wadannan mutanen ta kasance, haka take a kan irin wannan tsarin, fasaharsu ta kasance a kan irin wannan tsarin, sai Annabi ya yi musu magana a kan irin tsarinsu don ya bayyanar wa mutane da abin da Allah ya saukar musu da yarensu kuma da abin da suka sani.
Kamar fadin sa a cikin Hadisin Adiyyatus Sa’adi, cewa “ Fa’innal yadal Ulya – Hannu madaukakiya, Hiyal Mundiyyatu (Mu’udiyyatu) – ita ce mai bayarwa, Wal yadul sufla – hannu ta kasa, Hiyal Mundatu (Mu’udatu) – ita ce wacce aka baiwa”. Da fadin Annabi (SAW) cikin Hadisin Amiri, Manzon Allah (SAW) ya ce masa “Hal anka? (Sal amma shi’ita) – Tambayi duk abinda kake so?”.
Amma in aka duba maganganun Annabi (SAW) wadanda aka saba da su da fasaharsa sananniya da matattarar kalmominsa da hikimominsa wadanda aka ruwaito, hakika mutane sun wallafa manya-manyan littattafai a cikin wadannan maganganun nasa.
Yana daga cikin wadannan maganganun nasa abin da ba zai yiwu a yi kamanceceniya da su ba (a ce da maganar Annabi da ta wane iri daya ce) kuma ba a fito-na-fito wajen Balaga. Kamar fadinsa mai tsira da aminci cewa “Almuslimuna tatakafa’u dima’uhum – Musulmai jininsu tana kinantuwa (Ba jinin wanda ya fi na wani), dan karaminsu yana tafiya da alkawarinsu kuma hannunsu daya ne a kan wanda ba su ba.
Da fadinsa cewa “mutune kamar bakin talge ce (kurya) – Ma’ana mutane iri daya ce.