Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Amurka Joe Biden a birnin Lima, hedkwatar kasar Peru, inda suka yi musanyar ra’ayi mai zurfi cikin sahihanci, kan huldar kasashen biyu da harkokin kasa da kasa.
Yayin ganawar, bangaren Sin ya bayyana za a rungumi sahihanci da yin kokari wajen raya huldar kasashen biyu, tare da shugaba Biden, da kuma mai karbar ragamar mukaminsa, a daidai wannan lokaci da ake daf da mika mulkin Amurka ga sabuwar gwamnati.
- Xi Jinping: Alakar Sin Da Brazil Ta Kai Wani Muhimmin Mataki A Tarihi
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Yi Karin Haske Game Da Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka
A cikin shekaru 45 da suka gabata tun kafuwar huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, duk da cewa ana fuskantar sauye-sauyen yanayin duniya, Sin na nacewa ra’ayin cudanyar abota a maimakon kulla gaba da juna, da kuma cimma moriyar juna a maimakon haifar wa juna illa, kana da amincewa da banbancin ra’ayi, tare da kokarin cimma matsaya daya a maimakon yin takara ba bisa doka ba.
Shaidu na hakika sun bayyana cewa, Amurka ta matsa lamba, tana kokarin dakile bunkasuwar Sin bisa matsayinta na wai “mafi karfi a duniya”, ko da yake hakan ba zai cimma nasara ba ko kadan, a maimakon haka matakin ya illata moriyarta, kuma ya kara rura wutar fito-na-fito a duniya.
Sin da Amurka na da nauyi mai muhimmanci a bangaren kiyaye zaman lafiyar duniya, da kara azama ga bunkasuwarsu tare, don haka dole ne su yi kokarin ba da tabbaci, da amfani mai yakini ga duniya wadda ke fuskantar sauye-sauye da rikice-rikice.
Sin na fatan bangarorin biyu za su nace ga ka’idar mutunta juna, da zama tare cikin lumana, da haifar da moriyar juna, da kuma bin jagorancin da shugaba Xi Jinping ya gabatar, wato muhimman abubuwa 7 na raya huldar kasashen biyu, ta yadda za a daidaita huldarsu cikin lumana, don fitar da wata hanya da ta dace ta raya huldar sassan biyu, ta yadda hakan zai amfani kasashen biyu har ma da duniya baki daya. (Amina Xu)