Shugaba kasa Bola Tinubu ya tattauna da ‘yan jarida na kusan awa daya a ranar Litinin a gidansa da ke Legas. Wannan shi ne tattaunawarsa ta farko a kafafen yada labarai tun bayan da ya hau kan karagar mulki kimanin watanni 18 da suka gabata.
Muhimman batutuwan da aka tattauna sun hada da cire tallafin man fetur, kudirin sake lissafin haraji, sake fasalin tattalin arziki, fadin girman gwamnatinsa da kuma cin hanci da rashawa.
- Sojoji Sun Daƙile Harin Jirgi Mara Matuƙi A Yobe
- Babu Sauran Burbushin ‘Yan Ta’addan Lakurawa A Arewa Maso Yamma – Ministan Tsaro
A yayin da yake amsa tambayoyin manema labari, Shugaba Tinubu ya yi watsi da yadda ake sukar gwamnatinsa kan fadin girmanta, sannan kuma ya ce ba zai rage yawan majalisar ministocinsa ba.
“Ban shirya rage girman majalisar ministocina ba. Na ga muhimmancin hada su wuri guda. Ba na bai wa wani aikin da ba zai iya yi ba,” in ji shugaba.
Shugaba Tinubu ya kuma yi magana kan matsalar tsadar rayuwa a kasar nan. Ga miliyoyin ’yan Nijeriya, manufofin gwamnati, kamar cire tallafin man fetur da kuma kaiya darajar naira, sun jawo matsin tattalin arziki a Nijeriya.
Ya jaddada cewa ya yi abin da ya dace ta hanyar sanar da cire tallafin man fetur a bikin rantsar da shi a bara. “Ba na nadamar cire tallafin man fetur,” in ji shi.
Lakacin da aka tambaye shi ko gwamnatinsa za ta duba yuwuwar yadda za a shawo kan farashin kayayyaki don duba tsadar kayayyaki da ayyuka, shugaban na Nijeriya ya ce bai yarda da yadda gwamnati za ta kula da farashin kayayyaki ba. “Muna ci gaba da samar da harkokin kasuwa, muna aiki tukuru don samar kasuwanci mai dorewa”.
Ya kuma bayyana gamsuwarsa da yanayin tsaron kasar nan, sannan ya yaba wa hafsoshin tsaron bisa kwazon da suka yi wajen samar da tsaro a kasar nan. “Ina alfahari da abin da suke yi a yau,” in ji shugaban.
An gurfanar da tsofaffin manyan jami’an sojoji da suka hada da na sojan kasa da na sama, da kuma tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, wanda ya yi aiki a gwamnatocin baya, bisa zargin satar dukiyar al’umma a lokacin da suke kan karagar mulki.
Amma duk da haka, Shugaba Tinubu ya ce ba zai binciki duk wani shugaban tsaro ba. Lokacin da aka tambaye shi ko yana da shirin yin hakan. “Ba za ku raina cibiyar tsaro ba saboda barazanar bincike,” in ji shi.
Hakazalika, shugaban Nijeriya ya kuma yi magana kan kudirin sake fasalin haraji da ke gaban majalisar dokokin kasar. Ya ce gyaran harajin yana bukatar tattaunawa da rangwame, kuma kafarsa a bude take kan hakan.
Kudirin dokar dai ya fuskanci adawa mai zafi daga sassan arewacin kasar nan, musamman daga wasu gwamnonin da suka bayyana shi a matsayin kudirin da zai kashe arewa.
Sai dai kuma Tinubu ya ce babu gudu, babu ja da baya a kan kudirin sake fasalin haraji a Nijeriya.
Mista Tinubu ya kuma bayar da hujjar karbar bashin kudade daga cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya domin cike gibin kasafin kudin Nijeriya na shekarar 2025. Ya ce samun lamuni ba laifi ba ne, domin ana yin amfani da irin wadannan lamuni ne wajen bunkasa ababen more rayuwa a kasa.
Yayin da shugaban ya yi imanin ba za a iya kawar da cin hanci da rashawa ba, ya ce za a iya rage shi zuwa mafi kankanta tare da aiwatar da wasu hanyoyin za su hana faruwar hakan. Tinubu ya bayyana shirin rancen dalibai da tsarin biyan mafi karin karancin albashi da kuma cire tallafin man fetur a matsayin kokarin gwamnatinsa na hana cin hanci da rashawa.
Shugaban ya kuma zargi wadanda suka shirya rabon tallafi da hannu dumu-dumu wajen ibtila’in turmutsisin da ya faru a Oyo, Anambra, da Abuja, Babban Birnin Nijeriya. “Ina ganin wannan a matsayin babban kuskure daga bangaren masu shirya bayar da tallafin,” in ji shugaban na Nijeriya. Sama da mutane 60 da suka hada da kananan yara ne suka mutu a wanann lamari da ya faru a jihohin uku.