Sana’a wata hanya ce ta al’umma ke samun yadda za su tafiyar da harkokinsu na rayuwa ta yau da kullum,akwai sana’oi da yawa wadanda idan aka fara koyawa matasa su tun suna kanana, yin hakan ba karamain tasiri zai yi ba.
Domin kuwa abinda aka fara koyo tun cikin yarinta yana daukar hankali matuka da kuma girma cikin kaunar ita sana’ar da ake koyo.
- Hukumar NIS Ta Cafke Masu Safaran Makamai 3 A Kurus Ribas
- Manyan Kasuwannin Da Aka Fi Samun Goruba A Nijeriya
Sana’a tana sa wadanda suke yin ta su dogara da kansu ba sai sun je yin karamar murya ba, wajen wasu su nemi a taimaka masu cikin kaskantar da kai, maimakon haka ma watarana sune za su kasance masu taimakama wasu.
Sana’a tana sa kwanciyar hankali na wadanda ke yin ta, saboda da safe bayan sun tashi sun san inda za su nufa da kuma abinda za su yi.Akwai sana’oi wadanda aka gada daga Kaka da Kakanni na gargajiya kamar Rini, Saka,Jima,da sauransu suma idan aka koye su za a samu hanyar tsira da mutunci.
Sana’oin zamani kamar Walda,Kafinta, Gini, dinki da sauransu idan ana tura ‘ya’ya suna koya tun suna kanana za su tashi da nakaltar su fiye da yadda za ayi tunani, ba kuma za ayi amfani da irinsu ba wajen aikata abubuwan da basu kamata ba. Koyon sana’oi bai hana ‘ya’ya su rika zuwa makaranta, don haka kamata ya yi a rika koya masu sana’oi domin maganin zaman banza da sa kansu aikata abubuwan da basu dace ba.