• Leadership Hausa
Thursday, June 1, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Cutar Marburg A Ghana

by Idris Aliyu Daudawa
10 months ago
in Labarai
0
Cutar Marburg A Ghana
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Bayan da aka fuskanci annobar cutar Korona ‘yan shekaru da suka gabata ga kuma yadda kyandar Biri take kara saurin yaduwa sai kuma ga labarin bullar wata kwayar cuta mai tada hankali al’ummar duniya da gaske dake musabbabin kamuwa da Marburg.

Ita wannan kwayar cutar Marburg data bulla a kasar Ghana yammacin Afirka kamar yadda hukumar lafiya ta duniya ta bada sanarwar hakan.

  • Sabon Fim din JAMILA Zai Fara Haskawa A Makon Nan –Hafsat Sa’eed
  • ‘Yan Bindiga Sun Sace Yara 3, Sun Bukaci Kudin Fansa Naira Miliyan 100 A Jihar Kogi

Mutane biyu wadanda basu da alaka da juna suka mutu bayan an gwada su an gano sun kamu da cutar a kudancin sashen Ashanti na kasar kamar dai yadda hukumar lafiya ta duniya ta bayyana hakan, inda sakamakon gwajin da ma’aikatar lafiya ta yi ya nuna sun mutu ne sanadiyar cutar.

Cuta ce mai saurin yaduwa da kuma hadari tayi kama da cutar Ebola, wanda ya zuwa yanzu kuma ba wani rigakafin dake maganinta.

Jami’an lafiyar kasar sun yin iyakar kokarinsu wajen yin duk abubuwan da za su hana cutar yaduwa, yayin da hukumar lafiya ta duniya take taimakawa da jami’anta tare da kayan aiki zuwa kasar.

Labarai Masu Nasaba

Tallafin Mai: Ba A Cimma Matsaya Tsakanin Gwamnatin Tarayya Da NLC Ba

China Ta Yi Alkawarin Ci Gaba Da Kulla Alakar Tattalin Arziki Da Nijeriya

“Saurin daukar matakin da sahen kula da lafiya ya taimaka, ta yadda za a dakile yaduwar cutar, wannan shi ya dace domin da ace ba a dauki matakin ba, da cutar ta yi saurin yaduwa.

Darektan sashen na ofishin hukumar lafiya ta duniya dake kulawa da nahiyar Afirka Matshidiso Moeti ne ya bayyana hakan.

Abubuwan da suka kamata a sani dangane da kwayar cutar Marburg.

Marburg cuta ce wadda ta yi kama data Ebola wadda ta dade tana sanadiyar mutuwar mutane a yammacin Afirka shekaru masu yawa.

Jemagu masu bibiyar kayan marmari ke yada cutar ga mutane musamman ma wadanda suke aikin hadar ma’adinai.

Jemagun da suke dauke da kwayar cuta sune ke yada ta, kuma tafi cutar Ebola,sai dai masana ilmin kimiyya suna aiki tukuru domin hana yaduwar cuatar.

Da zarar mutum ya kamu da cutar ita kwayar cutar zata iya yaduwa cikin kankanen lokaci ta hanyar yaduwa ta wani abu mai ruwa-ruwa daga mutanen da suka kamu da ita, kamar Jini, Miyau da kuma Fitsari.

Kai har ma akan wasu abubuwa masu damsi kwayar cutar na iya makalewa.‘Yan’uwa da ma’aikatan lafiya sune wadanda za su fi saurin kamuwa da cutar, saboda kasancewar su da wanda ya kamu da cutar.

Tags: AnnobaBarkewaCutaEbolaGhanaKorona
ShareTweetSendShare
Previous Post

Muhimmanci Koya Ma ‘Ya’ya Sana’oi Tun Suna kanana

Next Post

2023: Dan Yayan Buhari, Fatuhu Muhammed Ya Fice Daga APC

Related

Tallafin Mai: Ba A Cimma Matsaya Tsakanin Gwamnatin Tarayya Da NLC Ba
Manyan Labarai

Tallafin Mai: Ba A Cimma Matsaya Tsakanin Gwamnatin Tarayya Da NLC Ba

5 hours ago
China Ta Yi Alkawarin Ci Gaba Da Kulla Alakar Tattalin Arziki Da Nijeriya
Labarai

China Ta Yi Alkawarin Ci Gaba Da Kulla Alakar Tattalin Arziki Da Nijeriya

6 hours ago
Za Mu Dauki Kwakkwaran Mataki Idan Gwamnati Ta Janye Tallafin Man Fetur —NLC
Manyan Labarai

Za Mu Dauki Kwakkwaran Mataki Idan Gwamnati Ta Janye Tallafin Man Fetur —NLC

7 hours ago
Akwai Wadataccen Mai Da Zai Ishi ‘Yan Kasa Nan Da Kwanaki 30 —NNPCL
Manyan Labarai

Akwai Wadataccen Mai Da Zai Ishi ‘Yan Kasa Nan Da Kwanaki 30 —NNPCL

8 hours ago
Tinubu Ya Gana Da Shugaban EFCC A Fadar Shugaban Kasa
Manyan Labarai

Tinubu Ya Gana Da Shugaban EFCC A Fadar Shugaban Kasa

9 hours ago
Kotu Ta Daure Basarake Shekaru 15 Saboda Garkuwa Da Kansa
Manyan Labarai

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Dakta Idris Abdulaziz

10 hours ago
Next Post
2023: Dan Yayan Buhari, Fatuhu Muhammed Ya Fice Daga APC

2023: Dan Yayan Buhari, Fatuhu Muhammed Ya Fice Daga APC

LABARAI MASU NASABA

Ya Dace ‘Yan Siyasan Amurka Su Yi Tunani Kan Kalaman Elon Musk

Ya Dace ‘Yan Siyasan Amurka Su Yi Tunani Kan Kalaman Elon Musk

May 31, 2023
Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Ta Samar Da Yanayin Da Ya Dace Na Tattaunawa Tsakanin Rundunonin Sojin Kasashen 2

Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Ta Samar Da Yanayin Da Ya Dace Na Tattaunawa Tsakanin Rundunonin Sojin Kasashen 2

May 31, 2023
Sin Na Son Hadin Kai Da Sauran Sassan Kasa Da Kasa A Fannin Nazarin Sararin Samaniya

Sin Na Son Hadin Kai Da Sauran Sassan Kasa Da Kasa A Fannin Nazarin Sararin Samaniya

May 31, 2023
Gudummawar Kasar Sin Ga Aikin Tabbatar Da Zaman Lafiya A Duniya Abu Ne Da Ake Gani A Zahiri

Gudummawar Kasar Sin Ga Aikin Tabbatar Da Zaman Lafiya A Duniya Abu Ne Da Ake Gani A Zahiri

May 31, 2023
Tallafin Mai: Ba A Cimma Matsaya Tsakanin Gwamnatin Tarayya Da NLC Ba

Tallafin Mai: Ba A Cimma Matsaya Tsakanin Gwamnatin Tarayya Da NLC Ba

May 31, 2023
Sin Na Goyon Bayan Gwamnatin Mali Wajen Yaki Da Ta’addanci Da Tabbatar Da Tsaron Kasa

Sin Na Goyon Bayan Gwamnatin Mali Wajen Yaki Da Ta’addanci Da Tabbatar Da Tsaron Kasa

May 31, 2023
An Gudanar Da Taro Karo Na 12 Na Dandalin Masanan Sin Da Afirka

An Gudanar Da Taro Karo Na 12 Na Dandalin Masanan Sin Da Afirka

May 31, 2023
China Ta Yi Alkawarin Ci Gaba Da Kulla Alakar Tattalin Arziki Da Nijeriya

China Ta Yi Alkawarin Ci Gaba Da Kulla Alakar Tattalin Arziki Da Nijeriya

May 31, 2023
Za Mu Dauki Kwakkwaran Mataki Idan Gwamnati Ta Janye Tallafin Man Fetur —NLC

Za Mu Dauki Kwakkwaran Mataki Idan Gwamnati Ta Janye Tallafin Man Fetur —NLC

May 31, 2023
Akwai Wadataccen Mai Da Zai Ishi ‘Yan Kasa Nan Da Kwanaki 30 —NNPCL

Akwai Wadataccen Mai Da Zai Ishi ‘Yan Kasa Nan Da Kwanaki 30 —NNPCL

May 31, 2023
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.