ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, November 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Muhimmancin Manufofin Sin Wajen Ingiza Ci Gaban Duniya

by CGTN Hausa
2 years ago
Sin

A bana ake bikin cika shekaru 45 da kaddamar da manufar kasar Sin ta aiwatar da gyare gyare da bude kofa. Gyare gyare da bude kofa ba kawai sun haifar da babban sauyi ne a kasar Sin ba, har ma matakin ya haifar da hadin gwiwar cimma moriya tare da sauran sassan duniya. 

A cikin shekaru 10 da suka gabata, Sin ta matsa daga matakin bude kofa mai nasaba da fitar da hajoji da matakan bunkasar hakan, zuwa bude kofa bisa dokoki, da ka’idoji, da jagoranci, da tabbatar da inganci, wanda hakan ke nuna yadda manufar “Bude kofa” ta zama muhimmin ginshiki na bunkasa ci gaban kasar.

  • Yarjejeniyar Zuba Jari Tsakanin Bangarori Daban Daban Da Sin Ta Gabatar Ta Samu Goyon Baya Daga Dukkanin Fannoni
  • Xi Ya Saurari Rahoto Daga Manyan Jami’an Gwamnatocin HK Da Macao

Budadden tsarin tattalin arzikin kasar Sin, ya kuma ba da gudummawa ga bunkasar tattalin arziki a matakai na zahiri. Har kullum Sin na kasancewa muhimmin jigo na ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya, wanda muhimmin ginshiki ne musamman a lokacin da yanayin farfadowar tattalin arzikin duniya ba shi da karfi sosai. Ga manyan kamfanonin duniya, suna cin gajiya daga bunkasar tattalin arzikin kasar Sin, tare da samun karin damammakin ci gaba a kasar Sin.

ADVERTISEMENT

Salon Sin na bude kofa, daya ne daga dalilan bunkasar tattalin arziki maras gurbata muhalli da na dijital. A shekarar 2022, sashen raya tattalin arzikin Sin na dijital ya kai kaso 41.5 bisa dari na GDPn kasar, wanda ya kai matsayi na 2 a duniya.

Ga misali, a nahiyar Afirka, tsarin amfani da fasahar sadarwa ta dijital wajen aikewa da sakwanni na Sin, ya taimakawa ‘yan Najeriya wajen yin sayayya ta yanar gizo cikin sauki. Tsarin fasahohin Sin na bunkasa ci gaba na dijital, yana amfanar jama’a dake sassan duniya daban daban, tare da ingiza sabon kuzari ga bunkasar tattalin arzikin duniya.

LABARAI MASU NASABA

Sin: Ya Zama Wajibi Japan Ta Janye Kalamanta Dangane Da Taiwan 

Li Qiang Zai Halarci Tarukan SCO Da G20 Tare Da Ziyarar Aiki A Zambia

Bugu da kari, kwazon Sin game da bude kofa, da himmarta wajen gina budadden tattalin arzikin duniya, ya samar da sabuwar mahanga ga tsarin jagorancin duniya. Har kullum Sin na nacewa salon tattaunawa mai zurfi, da gudummawar bai daya da cin gajiya tare, tana kuma maraba da dukkanin sassan duniya da su ci gajiya daga damammakin da take samarwa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin: Ya Zama Wajibi Japan Ta Janye Kalamanta Dangane Da Taiwan 
Daga Birnin Sin

Sin: Ya Zama Wajibi Japan Ta Janye Kalamanta Dangane Da Taiwan 

November 13, 2025
Li Qiang Zai Halarci Tarukan SCO Da G20 Tare Da Ziyarar Aiki A Zambia
Daga Birnin Sin

Li Qiang Zai Halarci Tarukan SCO Da G20 Tare Da Ziyarar Aiki A Zambia

November 13, 2025
Shugabar IOC: Gasar Wasanni Ta Kasar Sin Tana Da Babbar Ma’ana
Daga Birnin Sin

Shugabar IOC: Gasar Wasanni Ta Kasar Sin Tana Da Babbar Ma’ana

November 13, 2025
Next Post
Sanata Barau Jabril Na Kokarin Hana Shoprite Tashi Daga Kano

Sanata Barau Jabril Na Kokarin Hana Shoprite Tashi Daga Kano

LABARAI MASU NASABA

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma: Martani

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma: Martani

November 14, 2025
Kofin Duniya: Nijeriya Za Ta Fafata Da DR Congo A Wasan Ƙarshe

Kofin Duniya: Nijeriya Za Ta Fafata Da DR Congo A Wasan Ƙarshe

November 14, 2025
Masana’antu Masu Zaman Kansu A Arewa Sun Yi Maraba Da Harajin Kashi 15 Na Shigo Da Man Fetur

Masana’antu Masu Zaman Kansu A Arewa Sun Yi Maraba Da Harajin Kashi 15 Na Shigo Da Man Fetur

November 14, 2025
Ronaldo Na Fuskantar Dakatarwar Wasanni Biyu Bayan Samun Jan Kati

Ronaldo Na Fuskantar Dakatarwar Wasanni Biyu Bayan Samun Jan Kati

November 14, 2025
Editoci Sun Yi Gargadi Kan Rushewar Kafofin Yada Labarai Sakamakon Matsin Tattalin Arziki

Editoci Sun Yi Gargadi Kan Rushewar Kafofin Yada Labarai Sakamakon Matsin Tattalin Arziki

November 14, 2025
Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano

Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano

November 14, 2025
Abin Da Ya Sa NPA Ta Yi Hadaka Da ‘Snake Island Port’ -Dakta Dantsoho

Abin Da Ya Sa NPA Ta Yi Hadaka Da ‘Snake Island Port’ -Dakta Dantsoho

November 14, 2025
Shugaban NPA Ya Bukaci A Yi Hadaka Domin Cin Gajiyar Albarkatun Fannin Sufurin Afirka

Shugaban NPA Ya Bukaci A Yi Hadaka Domin Cin Gajiyar Albarkatun Fannin Sufurin Afirka

November 14, 2025
Bayan Barazanar Amurka: Sultan Ya Nemi Hadin Kan ‘Yan Nijeriya Wajen Yaki Da Ta’addanci

Bayan Barazanar Amurka: Sultan Ya Nemi Hadin Kan ‘Yan Nijeriya Wajen Yaki Da Ta’addanci

November 14, 2025
Jan Aikin Da Ke Gaban Manyan Hafsoshin Tsaron Nijeriya

Jan Aikin Da Ke Gaban Manyan Hafsoshin Tsaron Nijeriya

November 14, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.