Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bukaci ‘yan Nijeriya da su nemi sauyi ta hanyar dimokuradiyya maimakon zanga-zanga.
A wata sanarwa da shi da kan sa ya sanya wa hannu a ranar Juma’a 26 ga Yuli, 2024 a cikin mawuyaciyar rayuwa da ake ciki da kuma kiraye-kirayen nuna adawa da halin da ake ciki ta hanyar zanga-zanga, Sanata Kwankwaso ya jaddada cewa, za a iya samun sauyi mai inganci kuma mai dorewa ta hanyar karfin zabe.
“Da tsananin nauyin da ya rataya akaina nake bayyana ra’ayina game da halin da ake ciki a kasarmu Nijeriya, mun tsinci kanmu cikin wahalhalun da ba za a iya gujewa ba saboda shugabanninmu sun rasa wasu matakai tun 2007,” in ji
A ko da yaushe, lokacin gyara ba ya kurewa, za a iya dora kasar nan kan turba mai kyau don bunkasar tattalin arziki, wadata, da kyautata jin dadin ‘yan kasa.
Kwankwaso ya bayyana wasu rigingimu da suka samo asali daga rashin shugabanci na gari, kamar “yadda gwamnatin tarayya ta yi katsalandan a harkokin masarautun jihar Kano, da tsige mataimakin gwamnan jihar Edo, da rudanin siyasa a jihar Ribas, da rashin tsaro da ya addabi kasar nan baki daya.
“Sauran sun hada da rikicin siyasa a Jihar Kogi, zagon kasa ga matatar mai ta AIiko Dangote, takaddama game da yarjejeniyar auren jinsi (SAMOA), rikici tsakanin Sanata Ali Ndume da Shugabannin APC. Duk wadannan katsalandan ba dole ba ne, za a iya kauce musu.”
Ya kara da cewa, wadannan al’amura alamu ne na rashin bin ka’ida da kuma nuna gaskiya.
“Abin bakin ciki ne yadda rashin shugabanci na gari da son kai na shugabanni ya jefa ‘yan kasa musamman matasa cikin yunwa da rashin tsaro da kuma yanke kyakkyawan tsammani ga kasar.” in ji Kwankwaso.
Don haka, ya yi kira ga shugabannin Nijeriya a dukkan matakai da su gaggauta magance wadannan kalubale ta hanyar tabbatar da kyakkyawan shugabanci da bin doka da oda.
Da yake amincewa da kiraye-kirayen zanga-zangar da aka yi a baya-bayan nan, Kwankwaso ya amince da bacin rai da kuma burin ganin Nijeriya ta gyaru amma ya ja kunne kan illar da hakan zai iya haifarwa.
Ya bukaci ‘yan Nijeriya da su yi amfani da karfin kuri’unsu a matsayin makami mafi inganci wajen kawo sauyi.