Jiya Jumma’a, wata muhimmiyar takadar doka da kasar Sin ta bullo da ita, game da yankin Taiwan na kasar, ta jawo hankalin kasa da kasa, inda a ranar, wasu hukumomin kasar, ciki har da babbar kotun kolin kasa, da babbar hukumar koli ta gabatar da kararraki ta kasa, da ma’aikatar kiyaye tsaron al’umma, da ma’aikatar tabbatar da tsaron kasa, gami da ma’aikatar kula da dokokin kasa, suka wallafa “shawara kan yanke hukunci mai tsanani bisa doka kan masu tsattsauran ra’ayin ware Taiwan daga kasar Sin, gami da masu aikata laifin hura wutar rikicin kawo wa kasar baraka”. Kafafen yada labaran kasa da kasa sun nuna cewa, hakan ya kasance daya daga cikin matakai mafi tsauri da kasar Sin ta dauka, kan masu yunkurin ware Taiwan daga cikin kasar, tare da zummar taka birki ga yunkurin kawo wa kasar Sin baraka, gami da kiyaye dinkewar duk kasar baki daya.
Amfani da dokoki masu tsauri wajen yanke hukunci kan masu aikata laifin kawo wa kasa baraka, da kiyaye babbar moriyar kasa, abu ne da kasa da kasa su kan yi har kullum. Taiwan, wani bangare ne na kasar Sin, shi ya sa yanke hukunci mai tsanani kan wadanda suka aikata laifuffukan kawo wa kasa baraka, da hura wutar rikicin yin haka, ya dace da doka da hakikanin halin da ake ciki, kana, mataki ne da ya kamata a dauka, domin kiyaye cikakken ‘yanci, da hadin kai da dunkulewar yankunan kasar wuri guda. (Murtala Zhang)