Za a wallafa muhimmiyar makalar babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar, kana shugaban kwamitin kolin sojan kasar Xi Jinping, mai taken “Zurfafa aiwatar da juyin juya halin jam’iyyar kwaminis ta Sin”, a mujallar Qiushi fitowa ta 24, a gobe Litinin 16 ga watan nan.
Makalar ta nuna cewa, a cikin shekaru 10 na aikace-aikace, da bincike game da gudanar da cikakken tsarin mulkin jam’iyyar kwaminis ta Sin a sabon zamani, ana ci gaba da zurfafa fahimtar juyin juya halin jam’iyyar, da tara wadatattun darussan aikace-aikace, da samar da jerin muhimman nasarorin ka’idoji.
Makalar ta kara da cewa, “Ci gaban aikace-aikace, da kirkirar ka’idoji ba za su kare ba. Don haka ya kamata a tsaya tsayin daka kan raya karfin tunaninmu, da neman gaskiya, da tafiya tare da zamani, da yin kirkire-kirkire, da kuma ci gaba da gudanar da binciken aikace-aikace da kirkirar ka’idoji, ci gaba da zurfafa fahimtar juyin juya hali da jam’iyyar ta yi, da inganta ra’ayoyi da matakan juyin juya hali na jam’iyyar, da kuma aiwatar da juyin juya hali a kowane bangare da kyau”.(Safiyah Ma)