Jam’iyyar PRP ta bayyana cewa mulkin kama-karya ne ke sanya wawason kayayyakin abinci daga tireloli da rumbun ajiye a fadin kasar nan kuma zai iya shafar makoman Nijeriya.
A cikin wata sanarwa da mukaddashin sakataren yada labarai na jam’iyyar, Muhammed Ishak ya fitar, ya bayyana cewa idan har ba a dauki matakan da suka dace kan mummunan tsadar rayuwar da ke damun dimbin ‘yan Nijeriya ba, to kasar nan za ta fada mulkin kama-karya.
- Jam’iyyar ta bayyana hakan ne da take takaicin kan wawason kayayyakin abinci, musamman wanda ya faru a Dogarawa da ke yankin Zariya cikin Jihar Kaduna, inda mutane suka daka wawa kan tirelan da take dauke da taliya. PRP ta bukaci dukkan matakan gwamnati su kaddamar da shirye-shirye da zai kawo karshen matsalolin da al’ummar kasar nan ke ciki na mummunan yunwa da tsadar rayuwa.
Talla