Mai martaba Sarkin masarautar Gaya a jihar Kano Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulƙadir ya shaida cewa sauke su da aka yi nufin Allah ne, don haka ba su jin haushin kowa.
Masarautar Gaya guda ce daga cikin masarautun da tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa Sarki mai daraja ta ɗaya ce a shekarar 2020.
- Hukumomin Tsaro A Kano Sun Ƙi Biyayya Ga Umarnin Gwamnan Kano
- Jami’an Tsaro Na Ganawar Sirri Da Abba Da Sarki Sanusi II A Fadar Kano
A ranar juma’a ne dai majalisar jihar Kano ta warware dokar da ta gididdiba masarautar Kano zuwa masarautu huɗu.
Cikin wani rahoton BBC Hausa, Sarkin Gayan ya ce; Ai kowanne mutum abu kamar wannan ya same shi, ba zai ji dadi ba, amma Allah ne ya kawo haka, komai akwai lokacinsa.
“Allah ya rubuta da ma tun kafin a haife mu hakan za ta kasance, saboda haka mu bamu jin haushin komai.
“Wannan yin Allah ne mun karbe shi hannu-bibiyu,” in ji shi.
A cewarsa su ma su bin doka ne, kuma ba su ma bari awanni 48 sun cika ba, suka bi doka suka fita.
Sarkin ya ce fatansa ga masarautar Gaya da alummar Kano shi ne Allah ya ba su zaman lafiya da arziki mai dorewa kuma ya zaunar da su lafiya.
Bayan soke masarautun na Kano, bayanai sun nuna cewa gwamnatin jihar na duba yiwuwar majalisar dokokin jihar Kano za ta zauna ta yi nazari a kan duba yiwuwar samar da sarakuna masu daraja ta biyu.
Game da haka ne sarkin Gayan ya ce zai yi maraba da hakan kuma zai karbi wani tayin Sarki mai daraja ta biyu idan gwamnati ta yi masa hakan.